DALILAN DA SUKA SA AKE GANIN MA'AURATA A AFIRKA BASU IYA SOYAYYA BA

*DALILAN DA SUKA SANYA AKE GANIN MA'AURATA A AFIRKA BASU IYA SOYAYYA BA:
Yawancin aurataiya an daukesu a matsayin a kwanta a rash, a samu zuriya, a girma tare har mutuwa.
* Yana wuya kaga ma'aurata suna sumbatar juna a goshi ko a kumatu, kuma idan kaga sun rungume juna, toh labari mai dadi ne yasamu.
* Yana wuya kaga miji yana baiwa matarsa abinci a baki. Idan kaga hakan kuwa toh ka tabbata Matar ce batada lafiyar da ko lomar tuwo ba zata iya sanyawa ga bakinta ba.
* Idan ba a drama ba, idan kaga miji ya budewa matarsa kofar mota toh ka tabbatar kofar motor ce a 6ace.
* Abu guda daya dayake sanya magidanci a Afirka ya ta6a wuyar matarsa shine lokacin datayi korafin zazza6i yana damunta. Bazai kuma Kara ta6awa ba sai wani sabon zazza6in yazo.
* Lokaci daya ne zakaga miji ya dauko matarsa a hannu. Lokacin kuwa shine idan ta fara labour zai kaita asibiti.
* Idan kaga ma'aurata na zaune a waje da daddare, kada ka dauka tsabar soyayyace, fiya-fiya suka watsa a dakin suna jira warin ya ragu.
* Yawancin mata idan kaga sun sayasa mazajensu wani abu kyauta, toh ka tabbatar an kwantar da mazajen ne a gadon asibiti. Shine mai tausayi wai zakaga ta sayi lemo da ayaba na jaka.
* Idan kaga ma'aurata suna tsere-tsere, toh ka tabbata abun tsoro suka gani kowa yana ta kansa.
* Idan kaga ma'aurata tare sun fito da yammaci suna tafiya, bawai shawagi suka fito ba, yawanci togaciya zasu kai na wani ya daki dansu, ko kuma wani yawa yarsu ciki.
* Lokaci daya ne suke Wanka tare, Idan zasu fita aiki yazamana duk sunyi latti.
* Lokaci daya ne mata ke kallon idon mijinta dab da dab, lokacin dayake fada mata wani abu ya shiga idanunshi.
Abun haushi kuma shine:
A Nijeriya duk wanda yazama very romantic a wajen matarsa sai kaji suna cemar: "mijin Hajiya, Bawan Dudu, ko kuma tagama dashi"
Don Allah Afurkawa mu gyara.

Post a Comment (0)