DAN AREWA KA SHIGA TAITAYIN KA

'DAN AREWA KA SHIGA TAITAYINKA!
Tsohon shugaban kasar da alokacinsa yasa aka kwashe manyan kayan yakin rundinar sojin Nigeria daga arewa ya mayar dasu yankinsa domin a raunata arewa
Tsohon da a lokacinsa ne a shekarar 2006 bayan Mai Alfarma Sarkin musulmi Malam Muhammadu Maccido yayi tattaunawar sirri dashi kan matsalolin arewa, bayan sun kammala ya fito ya hau jirgi zai koma gida aka kifar da jirgin muka rasa Sarkinmu abin kaunarmu tare da wasu manyanmu na arewa, shin 'dan arewa bazaka hankalta ba?
A lokacin Sheikh Albaniy Zaria (Allah Ya jikanshi) yace dagangan aka dinga kifar da jiragen domin a raunata karfin arewa, shiyasa har yau basu fitar da sakamakon binciken abinda ya haddasa hatsarin jirgin ba
Tsohon da alokacinsa ne ya tattara sojojinmu masu ilmi kan tsaro, masu jarunta da hazaka da suka fito daga yankinmu na arewa yayi musu ritayar dole domin ya raunata arewa ta fuskan rashin wakilai a harkan tsaron kasar
Me wannan tsohon najadu makiyin arewa zai fada maka har kai 'dan arewa mai hankali ka biye mishi?
Wannan tsoho babu komai cikin kalamansa da yace kada shugaba Buhari ya sake tsayawa neman shugabancin kasarmu Nigeria a 2019 face bayyana tsananin sharrinsa da muguntarsa ga arewa.
Ina fatan 'yan uwana 'yan arewa zamu hankalta sannan mu fahimta
Yaa Allah Ka jikan Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido
Allah Ka tsaremu daga sharrin makiyanmu

Post a Comment (0)