MADIGO KO MA'AURATA?

MADIGO KO MA’AURATA:
Madigo Da Illolinta
Fatima Ahmad Buba

Hakika wannan babbar masifa ce da ta
shigo al’ummar Musulmi take kuma
habbaka kamar wutar daji.
Madigo – wata hanya ce ta biya wa kai
bukata da mata ke yi a tsakaninsu.
Hakika wannan halayya ta fi muni ga
Zina. Halayya ce da ko dabbobi marasa
hankali da tunani ba sa yinta. Madigo za
mu iya jefa shi a nau’in cutukan ruhi
wanda shaidan ke fesawa ‘yan Adam
gubarsa.
Neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin
Annabi Lut (a.s) wanda ya zo a tarihi
cewa Shaidan ne ya zo a siffar ‘yan Adam
ya nuna wa mutanen Annabi Lut (a.s)
yanda za su rika neman junansu. Shi ya
sa zuwan Musulunci ma ya kawo ma
hukuncin masu aikata wannan cewa kisa
ne ta hanyar jefo su daga dogon gini.
Hakika a shekarun baya ba za mu ce
babu wannan abu ba, amma ko da akwai
to akwai ya babu ne domin ba ka jin
hirarsa sosai. Amma yanzu me ya jawo
abin ya taso ya habaka har yana neman
samun gindin zama a kasashenmu na
Musulunci? Wannan tambaya ce da ta
rika kai kawo a raina inda har abun ya
kai ni ga bincike kuma cikin ikon Allah na
samo wasu amso shi da nake so na
fadakar da ‘yan’uwana Musulmi.
NA FARKO – Kaucewa koyarwa ta addinin
Musulunci da ya umarci iyaye da su aurar
da yaransu da wuri yayin da suka kai
minzalin balaga. Amma maimakon haka
sai muka dauka cewan hakan kauyanci
ne, don haka abar yara mata su yi karatu
mai zurfi. Ban ce ilmi mai zurfi ga mace
illa ba ne, domin ni ma daliba ce, amma
yanayin da ake barinsu ne yayin neman
ilmin yake da illa.
Misali saboda yarinya ana ganin ta girma
ta kai minzalin mutane sai iyaye su sakar
mata ragamar rayuwarta a hannunta ta
hanyar barinta ta yi shigar da ta ga dama
ta fita ta yi dinkin yayi, mai matse surar
jiki. Wayarta baruwansu da me ke cikinta?
Yaushe take da karatu yaushe ne babu?
Wane irin kawaye take mu’amala da su?
Komai an sakar mata yanda ta yi shi ne
daidai.
A irin haka tarar taron kawayen inda
masu irin halin sai su ja ta ai ta yi. Wasu
har gida za su rika biyo ta, ita uwa ta
saki baki ai kawayen ‘yarta ce don haka
sai a shigo a shige da ka ai ta yi. A irin
wannan ne za ka ga ita ma ta zama
gwana in ba a yi sa’a ba har kannenta ta
ba ta.
Na ga mutumin da matarsa ta bata masa
yarinyarsa da wannan abu. Ya auro
amarya bai san tana harkar ba yana da
yara sai babbar ‘yarsa take zuwa taya
amaryar kwana in ba girkinta ba ne an
zaci, shakuwace mai karfi a tsakaninsu
ashe abin da take koyawa yarinyar kenan
sai da abin ya shigi yarinyar ita ma ta
kware an kaita makarantar, kwana aka
kama su suna yi a nan ta ce matar
babanta ce ta koya mata. Wa iya
zubillah!
Sakacin Hukumomin Makarantu
Shi ma ya taka rawa wajen yaduwar
wannan mugun ta’annati a tsakanin yara
mata. Domin ba na mantawa muna
makarantar kwana an taba kama masu
wannan abu kawai sai aka kore su ba
tare da kwakkwarar bincike ba, wanda na
yi imanin ba su kadai ke wannan abu ba.
Da a ce hukumomin makarantun kwana
za su kafa kwararan matakai na tsaro a
dakunan kwanan dalibai. Sannan ya zama
wani maudu’i guda mai zaman kansa da
lokaci zuwa lokaci za su rika tunatar da
dalibai a kansa da illolinsa. Sannan in
suka kama masu yi su tsaya kyakkyawan
bincike kafin su zartar da hukunci to da
abin ya yi sauki kwarai.
Sakacin Hukumomi
Hakika hukuma tana babban sakaci a
cikin wannan al’amari domin dai da wuya
ka ji an ce ga matakin da hukuma ke
dauka domin magance wannan lamari.
Na san wasu za su ce hukuma ba sai ta
kama ba sannan za ta iya daukar mataki
a kai. To, gaskiya abin ba haka yake ba.
Dalili kuwa shi ne a yau hanya mafi
saukin yaduwar wannan badala shi ne
‘Intanet.’ Misali ka duba ‘Facebook’ ka yi
‘Searching’ kalmar ‘Lesbian’ kawai sai ka
ga guruf-guruf sun fi dari wadanda kawai
wannan abu ake a ciki. kuma abin bakin
ciki Hausawa ‘ya’yan Musulmi. Ba kunya
ba tsoron Allah za ka ga suna
maganganunsu na batsa, har da turo
hotunan juna kuma suna ajiye lamba, inda
mai bukatarsu.
Na san hukuma tana da ikon da za ta bi
numbobin da suka bude ‘Account’ na su
ta kamo su a ladabtar dasu amma ba ta
yi ba. Na biyu Akwai wasu shiri na cikin
‘Intanet’ da aikinsu kawai turo bidiyo na
wannan badala domin kara dulmiyar da
Musulmi wanda hukuma tana da ikon
toshe wannan shirye-shiryen, amma ta
dauke kanta a kan haka. Wannan suna
cikin abubuwan da suka taimaka kwarai
wajen yaduwar wannan cuta ta Madigo.
Mu sani duk da cewa Shaidan la’anannen
Allah shi ya kawo mana tallar wannan
masifa to amma fa a zamanin nan
yan’uwansa Yahudawa sun karfafa abun
ta hanyar jefo mana mugayen fina-finai
na batsa ta hanyar kasa kasai ko
tauraron ‘yan adam. Da intanet ta zama
ruwan dare kuma sai suka koma tura su
ta nan. Tun suna Turawa kyauta yau abin
ya zama da kudi ma ake siya ta Intanet
din saboda raja’ar da mutane suka yi
kansa.
Irin wannan finafinai zallar abin da suke
nunawa shi ne salo-salo na yanda jinsi
daya za su biya bukatarsu da juna cikin
sauki.
‘Yar’uwa mace bari ki ji hikimar
Yahudawa ta turo miki wannan balai.
1. Burinsu daya da Shaidan shi ne su
dulmiyar dake ga sabon Ubangiji. Domin
suna da sanin cewa ke ce uwar al’umma
don haka in kika lalace al’umma ta lalace
kuma duk al’ummar data dulmiya a sabo
to fa Ubangiji na dauke albarkarsa daga
wannan al’umma. Balai, zubar jini, fatara,
yunwa , cutuka za su yawaita a cikinta.
2. Babban burinsu a duniya shi ne rage
Musulunci don haka yayin da suka
kwadaita maki ‘yar’uwarki mace har kika
zama kina samun biyan bukatarki da ita
tofa a hankali sha’awar da namiji za ta
kau daga gare ki. Kin ga kuwa bake ba
haihuwa kenan. Wanda wannan wata
hanya ce ta rage Musulmi cikin sauki
domin dai sai da aure tsakanin namiji da
a mace ake samun haihuwa.
Matsalolin Madigo Ke Haifarwa Masu
Yinta
Wannan masifa ta Madigo na janyo
cutuka kala-kala marasa magani ga masu
yinta in ba su bari tun kafin ta riske su
ba.
1. Tana haifar masu da mugun ciwon
mara domin duk yanda suka kai ga
dabara da kwarewa ba za su taba inzali
kaman suna tare da namiji ba. Hakan
kuma yana nufin wannan ruwan yana
taruwa a mararsu a hankali yana
daskarewa har ya taru ya zame masu
ciwo mara jin magani.
2. Yana haifar da cutuka tun daga
farjinsu har izuwa mahaifarsu wanda shi
ma yana kashe masu sha’awa gaba daya
kuma yana iya hana haihuwa kwata-
kwata.
3. Yana iya haifar da cutar sida
(Kanjamau) ko kuma mugun ciwon nan
na hanji wanda yake haifar da gudawa ba
tsayawa sai dai ga mutum na tsiyayewa
kaman kudin guzuri.
Bayan wannan yana sanya ciwon ruhi.
Ciwon ruhi ba ciwone da ake sha masa
magani ko allura ba. Ciwo ne da yake
kekashe zuciya ya sanya imani ya fita
daga cikinta ya zamo dan Adam ya fita
daga haddin mutane yana kuma iya
aikata abin da dabbobima ba za su iya
aikatawa ba.
Ki sani ‘yar’uwa in an yaudare ki cewa
Madigo yana sanya arziki Wallahil Azim
karya ne. Domin Annabi (s.a.w) ya fada
cewa mazinaci ba ya taba arziki kuma
mun tabbatar da cewa Annabi (SAW)
baya fadar abu daga son zuciyarsa,
komai ya fada daga Allah (SWT). Don
haka ko kin gan su da kudin to ba
albarka ba kwanciyar hankali wanda su
ne jigon arziki.
Yar’uwa, ki yi a hankali da rayuwarki ki
san irin mutanen da za ki rika hulda da
su a makaranta ko wajen cinikayya ko
yanar gizo.
Duk yayin da da kika ga mace ‘yar’uwarki
tana yawan taba miki jiki, ko yabon jikinki
ko yawan yi miki kyauta mara ma’ana, ki
yi nesa da ita kafin ta dulmiyar dake cikin
masifar da ba za ki iya fita ba.
Malamai da iyaye da hukuma kunga
balain da al’umma take ciki abun ya wuce
kan ‘yan mata har matan aure dulmiyasu
ake a ciki. Don haka hakkinku ne ku tashi
ku fadakar ku ladabtar da mu, ko za a
samu rangwaman wannan masifa.
Ina fatan Ubangiji Madaukakin Sarki Ya
dube mu ba don halinmu ba, ba don
ayyukan mu ba, Ya yaye mana wannan
bala’i a tsakanin al’umma alfarmar
Sayyadina Rasulullah (SAW).
Tare da
Fatima Ahmad Buba (+989380996801)

Post a Comment (0)