GWAGWARMAYAR JARUMI AMITABH BACHCHAN

"GWAGWARMAYAR JARIMI AMITABH BACHCHAN"
.
KALUBALEN DA YA FUSKANTA
*************************************
.
Jarimi AMITABH BACHCHAN ya fuskanta qalubale dayawa na rashin NASARA a rayuwar shi kafin ya zama babban jarimi, Kadan daga cikin rashin nasaran da ya samu shi shine
.
Kafin jarimi AMITABH BACHCHAN ya shiga duniyar shirya fina-finai ta Bollywood, Shahararren jarimin yayi kokarin yin aiki awani gidan radio me suna 'ALL INDIA RADIO' amma suka ki amincewa da shi saboda munin muryar shi, Sukace basa bukatar irin muryar shi, Ko intabiyu ba ayimai ba sukayi watsi da shi.
.
Alokacin da jarimi AMITABH BACHCHAN yafara zuwa garin Mumbai na farko domin shiga masana'antar film, Besan kowa ba agarin Mumbai, bema san inda zejeba domin ya kwanta, A dalilin hakane ya yanke shawaran kwana agefen titi, Jarimi AMITABH BACHCHAN Yasha kwana agefen-titi acikin garin Mumbai.
.
Jarimi AMITABH BACHCHAN anki amincewa dashi alokacin da ya nemi abashi dama na zama jarimi a film amma aka ki amincewa da shi, Producers sunsha gayama jarimi AMITABH BACHCHAN cewa yayi TSAYI dayawa sannan bashida KYAUN da ze iya zama jarimi, saboda haka yakamata ka hakura da burin zama jarimi, Amma duk da haka jarimin yaki hakura.
.
A shekara ta alif (1969) ne jarimin ya samu nasaran fara zama jarimi da film din sa mesuna 'SAAT HINDUSTANI' jarimi yayi nasaran lashe lambar yabo na farko arayuwasa da wannan film din, Inda jarimin ya samu lambar yabo na 'SABUWAR FUSKA' wato (NATIONAL FILM AWARD FOR BEST NEWCOMER da wannan film din da ya farayi.
.
Jarimin yacigaba da fuskantar matsaloli arayuwarsa kafin ya zama babban jarimi, Jarimi AMITABH BACHCHAN yayi shekaru 8 (takwas) yana gwagwarmaya domin yazama babban jarimi.
.
Tun daga shekara ta alif (1969) zuwa Shekara ta alif (1973) jarimi AMITABH BACHCHAN yayi fina-finai 12 ajere duka suna faduwa, Alokacinne yayi wani film me suna "ZANJEER" inda film din ya zama Hit, Daga nanne jarimin yaci gaba da samun nasara arayuwarshi.
.
A shekara ta alif 1984 jarimin ya dakata da harkan film, Inda jarimin ya shiga SIYASA, Bayan jarimin ya shafe shekaru 3 (uku) yana gwagwarmayar SIYASA daga nanne jarimin yabar harkan SIYASA, Jarimin yacigaba da fuskantar matsala arayuwarshi, inda jarimin ya samu matsalar karayar arziki, daga nanne jarimin yayi ritaya na dan wani lokaci a harkan film, awannan halin da ya tsinta kansa ne na karayar arziki jarimi AMITABH BACHCHAN ya nema babban mai bada umurninnan me suna YASH CHOPRA da yabashi aiki, adalilin haka YASH CHOPRA yasa jarimi AMITABH BACHCHAN acikin film dinnan me suna MOHABBATEIN wanda akayi a shekara ta (2000).
.
Wannan hoton shine hoton da jarimi AMITABH BACHCHAN yasa a takardan application din sa na neman aiki a masana'antar film na Bollywood a shekara ta alif (1968) zuwa shekara ta alif (1969) Jarimin yasa hoton ne ashafin na Instagram yana yiwa kansa wasa da dariya.
.
Ga abin da Babban jarimin ya rubuta ashafinsa na Instagram:
“My application picture for a job in movies .. 1968.. no wonder I was rejected !!”
.
Jarimi AMITABH BACHCHAN yanzu haka ya kwashe kusan shekaru 50 yana aiki a masana'antar Bollywood, Kuma ya samu NASARORI masu yawa arayuwarshi.
.
He tweeted: “T 2617 - Job Application : Name : Amitabh Bachchan DOB : 11.10.1942, Allahabad Age : 76 yrs Credentials : worked in films for 49 years , IN APPROX 200 FILMS Speaks ; Hindi, English, Punjabi, Bengali HEIGHT : 6’2’’ .. Available .. YOU SHALL NEVER HAVE HEIGHT PROBLEM !!!”
.
Yanzu haka jarimi AMITABH BACHCHAN yana shooting din film din su me suna 'THUGS OF HINDOSTAN' inda za muga jarimin tareda jarimai irinsu
.
*Aamir Khan
*Katrina Khaif
*Fatima Sana Shaikh

Post a Comment (0)