KASHE KAI
Da Sunan Allaah Mai Rahma Mai Jin Kai.
Haqiqa Shi rai Abu ne mai Matukar Muhimmanci, ko kuma ma ince yana daga cikin Abubuwa Mafi Matukar Muhimmanci ga wadanda suka san Muhimmancin nasa.
Tun daga Lokacin Da na fara wayo, na sha jin Labarai iri Daban-Daban dangane da irin mutanen nan masu kashe kawunan su ta Hanyoyi iri Daban-Daban kuma bisa Mabanbantan Dalilai. Zakaji wani ance ya rataye Kanshi, Wata tasha Piya-Piya, wasu Shayin Bera wasu kuma sun fada ruwa sun mutu. Sai dai abinda yafi Tsaya min a Raina a duk lokacin da na ci karo da irin wannan labarin, wasu Tambayoyi ne da suke da Wuyar samun amsa tunda bani da ikon ganin wadanda suka aikata irin hakan bare na tambaye su. Ga wasu daga cikin irin wadannan Tambayoyin;
1. Shin masu aikata irin wannan Ta'asar wane irin tunani suke da shi ne?
2. Shin Ina Imanin su ya tafi ne?
3. Me yayi zafi ne haka?
Duk da nasan cewa ba zan samu Damar Ganawa da ko dayan su ba balle in mishi wadannan tambayoyi, ana Bincikawa zaka taras cewa dalilan da ke sa mafi yawancin su suke kashe kawunan nasu Dalilai ne masu Matukar Ban Al'ajabi, Takaici da kuma daure kai.
Misali, na taba karanta labarin wani wanda ya kashe kansa a cikin Jaridar Aminiya Kawai saboda an hana shi auren wacce yake so. To sai me don an hana ka ita? Ka manta Hausawa na cewa matar mutum Kabarin sa? Ko ka manta ne cewa Allaah Shi ne yake Zabawa Kowannnen mu abokin zamansa? Yanzu bayan wannan al'amarin ya faru an dade da yawa ne ayi wata shida ita kuma tayi auranta ko kuma ma ta manta dakai, kai kuma in Kaje gaban Ubangiji wacce amsa ce kake tunanin zata kubutar dakai daga azabar sa?
Haka wata itama da naji labarin ta sha Piya-Piya saboda an hana ta auran wanda take so, Allaah Ya taimake ta bata mutu ba Allaah Ya ba Likitoci dama suka ceto rayuwar ta bayan ta sha wuya. In kika tafi kina Tsammanin hakan zai Hana shi auran wata ne? To ke MECECE Ribar ki ma in hakan ta faru? Watakila ma mata hudu zai yi ya manta da ke kina can kina shan tambayoyi shi kuma yana nan ya a Watayawa abinsa.
Yaku 'Yan uwana musulmai, Lallai ne mu sani cewa Allaah da ya bamu rai da lafiya yafi kowa sanin irin halin da muke ciki, kuma Shi Ke Da maganin duk wata damuwa ko bukatar dake cikin ran mu, sannan Shi ne ya ce mu roke Shi zai amsa mana. To me zai Hana mu Rungumi Kaddarar da duk ta same mu Mukoma gare Shi?
Allaah Ya Shiryar Damu Hanya Madaidaiciya Kuma Ya Azurta Mu Da Kyakkyawar Fahimta. Aameen Thumma Aameen.
© 2018
*_Haiman Raees_*
_*Phone:*_
08185819176
_*Web:*_ www.haiman.com.ng
_*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
_*Twitter:*_ @HaimanRaees
_*Instagram:*_ Haimanraees
_*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com