FALALAR GEMU

TAMBAYA
========
👇
Asslm  alykm wrhmtull malam barka da kokari  Dan Allah ayita hakuri da mu bamuda abinda xamuyimka mu sakama da abinda kk mana bancin addu a fatan Allah yasadamu a aljanna ameen 1, da malam gameda geme inaso ayiman bayanin falalarsa 2 da ina xuwa inane geme yake farawa kuma a ina yake karewa duk wani gashi dayafitima a kasan baki da gefin fusaka gemeni ko xaka iya debeshi nagode inaso nayi koyi da annabi ba ragi ba kari acikin ajiye gemu tareda cewa acikin kumai ina sun hakan ngd.

AMSA
=====
👇
1. Na farko dai ajiye Gemu wajibi ne a bisa karantarwar manzon Allah saw, sannan ya isheka falalarsa kawai ace da kai manzon Allah saw yana dashi, Sannan Manzon Allah din yana taje gemunsa kuma yana umartar mutane hatta a mimbarin jumu'ah da suke taje gemunsu, sannan da gemu aka binne manzon Allah saw. Harma Kuma yana cewa KUNA CIKA GEMUNKU KUNA RAGE GASHIN BAKINKU, sannan ya tabbata lokacin da Ashsheik Mal Usaimin yana jinya, a lokacin da gashin jikinsa yana zubewa, da ya fahimci kamar gashin gemunsa zai iya zubewa sai yayi addu'ah cewar Allah yasa ya mutu kafin gemunsa ya zube, domin yana jin kunyar Haduwa da Annabinsa Alhalin bashi da gemu, nan da nan Allah ya karbi Ransa kafin gemunsa ya zube.

2. Gemu yana farawa daga haba zuwa makogwaro zuwa kumatu har zuwa inda gashin kai yake hadewa dashi.
  Rageshi kuma, wasu suna ganin idan ya kai kamar dani biyu, zaka iya rage abinda ya wuce haka.
  Sannan jan hankali ga mutane, duk da cewar gemu wajibi ne barinsa, idan har aka bata masu gemu a wajenku, Aka jefesu da ta'addanci ya zama siffa ce ta wasu da suke yin ta'addanci, wanda kai kanka zaka zama abin zargi idan ka ajiye gemu, ko mutane zasuke gudunka ko suna zargin masu gemu ko kai kanka da cewar duk mai gemu dan ta'adda ne ko kuma ma hukuma zasu iya kamaka a kaika wani wuri ana ta tuhumarka, to anan maganar gaskiya zaka iya Askewa, dan ka tsira da addininka da mutuncin ka a cikin mutane.

Allah shine masani


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)