MACEN DA KE ZINA AMMA TA TUBA YA ZATA YI DA KUDIN?

TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum Malam dafatan kana lfy allah yabaku ladan aikinku na alhairi Malam tabbayata shine wata yayatace abaya tana zina har tasayi Kayan sawa tasayawa iyayenta kuma suna ibada dakaya kai harda itakanta tana sallah dashi to yanzu ta tuba tabar yin zina kuma batada sana ar yi indai tana zaune zata Iya koma aikin zina don tasamu kudin Sabulu da sauran bukatunta da yaranta marayu guda uku shine ta tambayi wani malamin shin kudinta da tara nazina yakai dubu 40 shine takeso tahada dawani kudin taja jari don rufin asirinsu sai yace yahallata data gayamin nace bari nayi bincike cikin lamarin daga gurin malaman sunnah.

AMSA
======
👇
Ya halatta tayi kasuwarta da wannan kudin, tinda har ta tuba.
Allah yace فمن جاعه موعذةمن ربه فنتهافله ماسلفى وامره الئ الله.
  wato duk wanda wa'azi yazo masa daga ubagijinsa, sai ya dena to Al'amarinsa yana wurin Allah.
   sabida haka babu lefi tayi kasuwa da kudinta.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Post a Comment (0)