YADDA AKE YIWA JARIRIYA KO JARIRI ADDU'A YAYIN KHUTUBA
TAMBAYA TA 2904
***************
Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarkatuhu!!!.
Da fatan Malam yana lafiya Allah yasa Ameen
Malam nine aka yiwa haihuwa wane irin tsari ne wanda Musulunci ya tanadar na wajen yiwa jaririyar huduba?
AMSA
***
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Ita dai khutbah ana yinta ne aranar da aka haifi jariri ko washegari, ko bayan kwana uku da haihuwarsa. Da farko zakayi mata tahneek (wato ka tauna dabino mai zaqi, sannan ka goga mata shi acikin dasashinta).
Sannan kayi mata kiran sallah a kunnenta na dama, iqamah kuma akunnenta na hagu, Sannan ka ra'da mata sunanta, sai kuma addu'o'in da zaka tofa mata akanta da fuskarta kamar fatiha, ayoyi hudu na farkon baqara, ayatul kursiyyi da ayoyi biyu na bayanta, sannan ayoyi uku na karshen Suratul baqarah.
Sai kuma Suratul Ikhlas da Falaq da Nas Qafa uku-uku. Sai kuma addu'o'in da suka zo acikin hadisai kamar :
أُعِيذُك بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لَامَّةٍ
U'eedhuki bi kalimaatil Laahit taammati min kulli shaytaanin wa haammatin, wa min kulli 'aynin laammatin. (Qafa uku zaka tofa akan fuskarta)
FASSARA : ina nema miki tsari da albarkar kalmomin Allah cikakku, daga sharrin duk wani shaidani da baqin ciki, (kuma ina nema miki kariya) daga duk wani ido abin zargi.
Idan kayi mata wannan In sha Allahu zata aamu kariya ta musamman daga Allah, daga dukkan wani shaidani ko masu kambun ido, harma duk wani abinda zai chutar sa rayuwarta.
Ranar suna kuma zaka yanka mata rago guda daya. Kayi sadaqah da naman (kamar yadda yazo a sunnah).
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990