*_Tambaya ta (416)_*
:
_Menene hukuncin Sallar Matar da bata rufe *Duga-Duganta* ba kokuma wani Sashe na jikinta ya bayyana tana *Sallah?*_
:
*_Amsa:_*
:
_Abinda yake wājibi akan Mace idan zātayi *Sallah* shine, dōlene ta rufe dukkan jikinta da tufāfi in banda fuskarta dakuma tāfukan hannāyenta, domin ita *Mace* dukkaninta al'aurace inbanda wajen da aka tōgace, idan kuwa har wani ɓangare na jikinta yabayyana kamar *Gāshin-Kanta, Ƙwabrinta,* ko wani sāshe na jikinta, to *Sallarta* bata ingantaba, domin kuwa *Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ)* Yāce:_
:
*"لا يقبل الله صلاة حائض إلا بخمار"*
*_MA'ANA_*
*_Aʟʟāн(ﷻ) bāya karɓar Sallar Mātar da (ta balaga tafāra) Haila sai (in tā lulluɓe kanta da jikinta) da mayāfi,_*
:
_To amma dangane da abinda yashāfi hukuncin fitowar *Dugā-Dugan-Mace ko Ƙafāfunta* acikin Sallāh anan *Mālamai sunyi Saɓāni,* Mazhabobin *Mālikiyya, Shāfi'iyya, Hanābila* da wani sāshe na Mazhabin *Hanafiyya* tāreda mafi yawa daga cikin *Mālamai-Ma'abōta-Ilimi* duk suntafine akan cewa wājibine *Mace* ta suturce *Dugā-Duganta* idan zātayi Sallāh, kuma sunkafa Hujjarsune da *Hadīsin Ummu-Salama* wanda tayiwa *Aηηαвι(ﷺ)* tambaya cewa:_
:
*"أتصلي المرأة في درع وخمار ليس عليها إزار؟ قال إذا كان الدرع سابغا يغطي ظهور قدميها"*
*_MA'ANA_*
*_Shin Mace zāta iyayin Sallah acikin mayāfi da doguwar riga ba tāre da tāɗaura zane ba? Sai Aηηαвι(ﷺ) Yace eh idan yakasance rigar yalwatacciyace zata iya sauka har ƙasa ta lulluɓe bayyanar Dugā-Duganta:_*
:
_Wato abin fahimta anan shine, kenan idan har tufāfin bazai iya sauka har ƙasa ya lulluɓe *Dugā-Dugantaba* to Sallah batayiba kenan saboda barin wancan *Sharaɗin* da'akayi,_
:
_Saidai wani sāshe na Mazhabin *Hanafiyya* suntafi akan cewa ba dole bane sai Mace tarufe *Dugā-Duganta* a Sallah ba, sukace *Dugā-Dugai* ba al'aura bace, domin abune dayake yawan bayyana ajikin Mace in tana cikin gida, sannan sukace bābu wani Hadisi da ya inganta daga *Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ)* da yace dole sai Mace tarufe *Dugā-Duganta* a Sallah, sukace wancan Hadisi da aka kafa *Hujja* dashi akan wajabci, sukace Hadisine *Mauƙūf,* duk maruwaitansa sun tsayane akan *Ummu-Salama* basukai ga *Aηηαвι(ﷺ)* ba, danhaka sukace *Fuskar-Mace da Tāfukan-Hannayenta, da Dugā-Duganta* duk ba al'aura bane acikin Sallah, amma zāsu iya zama al'aura idan ba acikin *Sallah* bane,_
:
_To amma Saidai magana mafi inganci kamar yadda mafi yawan *Mālamai* suka rinjāyar da'ita shine, wājibind *Mace ta lulluɓe* ko ina ajikinta idan zatayi Sallah, saidai in bata sāmu tufāfinda zata lulluɓe jikinta dashiba, to anan sai ayimata uzuri, domin kuwa akan iyayin Sallah tsirārama idan anrasa tufāfi, hakanan kuma idan Mace tā ɗauki lokaci mai tsawo tana Sallah batare da tana lulluɓe dukkan jikintaba sakamakon batasan cewa lulluɓe jiki a Sallah wajibi bane, wasu *Mālaman* suna ganin cewa dolene sai ta rāma waɗancan *Sallolin,* to amma magana mafi inganci bazāta rāmasuba, domin itama anan za'a yimata uzurine da *Jāhilcinta,* danhaka baza ace dole sai tā rāmasuba, saidai tayi ƙoƙarin gyāra na gaba kawai,_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*_→AMSAWA←_*
*Mυѕтαρнα Uѕмαn*
*08032531505*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
*_↓↓↓_*
:
*"عـون الـمـعـبـود" (2/242)*
:
*"مـعـالـم الـسـنـن" (1/159)*
:
*"الـشـرح الـمـمـتـع" (2/161)*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*Daga Zaυren*
*Fιƙ-нυl-Iвādāт*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi