TAƘAITACCIYAR HUDUBA



TAƘAITACCIYAR HUDUBA

Dukkan Godiya ta Tabbata Ga Allah Ubangijin Dukkan Ababan Halitta...

Ubangijin Sammai Da Kassai...

Ubangijin da Babu wani bu daya isa yaru saida izninsa...

Yaku Yan uwa musulmi musani cewa Allah bai halicci mutum da Aljan ba saidan Mu Bauta masa...

Amma duk da haka munshagaltu da Bautar wasun Allah, 

a) Akwai masu Bautar kansu:-

Mai Bautar kansa shine wanda bai damu da dokar Allah ba sai binda zuciyarsa ta umarce shi kawai yake aikatawa...

 Idan aka kira sallah bai damuba sai zuciyarsa tace yaje sannan zaije sai zuciyar ta yarda sannan zai aikata alkhairi...

Baya wani aiki saida umarnin zuciyarsa.
Yabar Umarnin Allah da Manzon sa...

b) Akwai masu Bautar mutane:-

Mai Bautar mutum shine wanda baya wani aiki saida umarnin Sarki ko Dan siyasa...

Bazai iya zuwa ga sallah ba ko kyauta ko sadaka saida umarnin mai gidansa...

ko Malaminsa yace yayi sadaka sannan zaiyi sadaka, bazaiyi sadaka haka kawai saboda Allah yace ayi sadaka ba...

Baya salati yadda Annabi {s.a.w} yakoyar sai irin wanda malamin sa yakoyar dashi...

Baya sallah irinta Annabi {s.a.w} sai irin wacce malamin sa yakoyar dashi...

c) Akwai Masu Bautar Dukiya:-

Mai Bautar Dukiya shine ma'aboci son dukiya saboda kasuwanci baya sallah akan lokacinta...

Saboda dukiyar kada taragu baya iya fitarda zakka...

Saboda Kada kafishi da arzuki bazai iya baka zakka a dunkule ba saidai ya tsinkata gutsi-gutsi...

Saboda bakin ciki yasan bakada abinci a gidanka amma saiya biya maka kujerar Hajji amaimakon ya baka kudin ka kula da iyalanka...

Baya iya bacci saboda tunanin Dukiya...

Ya kewaye gidansa da tsaro saboda tsoran barayi yamanta Allahn daya bashi dukiyar shine wanda zai kula masa da ita...

Baya iya taimakon Addini da ita saboda soyayyarsa da dukiyar. Lallai lokaci zaizo zaka mutu kabarta...

d) Akwai Masu Bautar Mata:-

Basa iya aikata komai saida umarnin matansu...

Basa iya kyautatawa iyayensu saida sai matansu sun basu umarni...

Basa iya taimakon yan uwansu sai matansu sun basu umarni...

Basa iya fita sallah saida umarnin matansu...

Basa iya zakka ko sadaka saida umarnin matansu, sunbar umarnin Allah sunkoma bin umarnin matan su...

Duk wani aikin Alkhairi basa iyashi saida umarnin matansu...

e) Akwai Masu Bautar Abin Hawa:-

Suna son abin hawansu fiyeda soyuwarsu da Allah da manzon sa...

Matar makwabcinka babu lafiya bazaka iya bada motarka akaita Asibita ba, saboda sonkada motar...

Idan motarka ta sami matsala baka iya nutsuwa saika kaita angyara amma idan mahaifiyarka batada lafiya saikaga dama zakaje gareta...

Ka chanja abokai saboda kanada mota a yanzu...

Ka chanja iyaye kana jingina da iyayen wasu saboda kanada mota...

Kabar Yan uwanka suna wulakance saboda kanada mota...

Kafi damuwa da motarka fiyeda sallah a jam'i...

f) Akwai Masu Bautar Bokaye da malaman Tsubbu:-

Baka yadda da Kaddara ba sai abinda malamin tsubbu yafada maka zakai...

Dakaji ciwon kai saika rinqa tunanin wanine yamaka asiri...

Daka rasa wani abu a dukiyarka saika fara cewa anjefeka...

Kamanta da cewa Allah ne yabaka dukiyar...

Malamin tsubbu zaice ka aikata sabo komai girmans dan samin duniya ko kada karasa kujerarka ta mulki ko office ko sarauta, kuma kabi umarninsa kamanta da Allah ne ke bada mulki...

g) Malamai Masu Bautar Ruhanai:-

Basa aikata komai saida umarnin Ruhanai...

Hatta sallarsu takoma saida Iznin Ruhani...

Basa yin wata ibada ko yanka saida iznin Ruhanai...

Basa yin sadaka saida iznin Ruhanai...

Hatta iyalansu basu kusantar su saida yadda Ruhanai suka umarcesu suyi...

Basa saka sutura sai wacce Ruhanai suka Umarce su...

Basa amfani da turare sai wanda Ruhanai suka Basu izni suyi amfani dashi...

Yaa Allah kaine wanda ka halicce mu kace mu bauta maka da gabban mu guda Bakwai (7) muyi maka sujjada dasu...

Allah kada kabarmu muyi aiki dasu ga umarnin wanin ka sai kaikadai ya Allah...

Yaa Allah muna neman taimakonka acikin dukkan ibadun mu...
kada kabarmu muyi abinda zuciyar mu ta raya mana...

Kabamu ikon bauta maka kai kadai ka shiryar damu hanyarka irin hanyar da shiryar da Sahabban Manzon ka {s.a.w} Ameen...

Yaa Allah dukkan mai wata buqata ta Alkhairi Allah kabiya masa...

Marasa lafiyar mu Allah kabasu lafiya...

Wanda suka mutu suka koma gareka yaa Allah ka azurtasu da Rahmarka kasaka su acikin Aljannarka madaukakiya Aljannah fiddausi...

Masu auren mu Allah ka tabbatar musu da zaman lafiya da Qaunar juna a tsakaninsu...

Wanda basu da Aure Allah ka azurtasu da abokan zama nagari masu cike da tsoran Allah da koyi da sunnar Manzon Allah {s.a.w}...

Allah ka gafarta mana dukkan zunubanmu...Ameen
Post a Comment (0)