*_Tambaya ta (409)_*
:
_Menene hukuncin satar *Wutar-Nepa ko Ruwan-Fanfo kokuma Network kamar Wi-Fi* da sauransu??_
:
*_Amsa_*
:
_*Ko Shakka bābu* wannan tambayace mai matuƙar muhimmanci, domin ayau anwāyi gari Mutāne da yawa sukan halattawa kansu amfāni da dukiyar datake ba mallakarsu bace, *Alal-Hakika* dukkan *Mālamai* sunyi *Ittifāƙin* cewa harāmunne wani Mutum yabi wata *ɓarauniyar hanya* yasāci dukiyar datake ta *Al-Ummāce* gaba ɗaya, ko tawani *Company* kokuma tawasu *ɗai-ɗaikun Mutane* da suka mallaketa, kamar irin su:_
:
_*Wi-Fi,*_
*_Network,_*
*_Wutar-Nepa,_*
*_Ruwan-Fanfo,_*
:
_Da sauran makamantansu, dayawa Mutane sukanyi amfani da wasu hanyoyi mabambamta wajen aikata irin wannan nau'i na *māguɗi,* wasu kaitsaye suke *Sātar Wutar-Nepa* ta ɓarauniyar hanya batare da sanin hukuma ba, yayin da wasu kuma sukanyi wani *māguɗine* acikin *Nā'urar* dake lissafin adadin abinda sukayi amfani dashi na *Wutar-Nepa* ko *Ruwan-Fanfo,* sai Mitar tariƙa rage yawan abinda aka *zūƙa* na *Wutar,* kamar inda misali anyi amfani da nauyin abinda yakai *(100%)* sai Mitar tanuna cewa baifi *(50%)* ba ko kasa da haka, kokuma masu bin wata *ɓarauniyar hanya* suna amfani da *Network* irin na *Wayar-Salula* su Sāci wani adadi mai yawa na *Data (MB/GB)* kokuma *Credit* na kiran waya suna amfani dashi ba bisa *ƙā'ida* ba, to su sani cewa dukkansu haramun sukeci, to amma dangane da abinda yashafi *WI-FI* akwai waɗanda suke barin *WI-FI* ɗin abuɗe dan amfanin jama'ar da sukazo wajen, to idan Mutum yasan dahakan ya halatta yayi amfani dashi, amma wasu guraren sukansa *Password* sukulle kayansu, to koda Mutum yasan *Password* ɗin indai ba masu gurin bane suka bada izinin abashi, to haramunne yabuɗe yayi amfani dashi, domin *Aʟʟαн(ﷻ)* Yana cewa:_
:
*"يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَأْكُلُوا أَمْوَالَكُم بَيْنَكُم بِالْبَاطِلِ إِلَّا أَن تَكُونَ تِجَارَةً عَن تَرَاضٍ مِّنكُم،،،،،،،ْ''*
*_MA'ANA:_*
*_Yā waɗanda kukayi Īmāni da Aʟʟαн(ﷻ) kada kuci dukiyoyinku ta hanyar ɓarna (haram) saidai ta hanyar cinikayyar dakukayi yarjejeniya atsakāninku,,,,,,_*
:
_Danhaka abune sananne ga dukkan wanda zaija *Wutar-Lantarki ko Ruwan-Famfo* to dama akwai yarjejeniya tsakaninsa da hukuma cewa duk wata zai riƙa biyan wasu *kuɗāɗe,* danhaka bai halattaba Mutum yawarware wannan alƙawarin ta hanyar *Sāta, Māguɗi, Yaudara, Algus,* kokuma haka kawai Mutum yaƙi biyan kuɗin da gangan, duk bai halattaba, saboda *Aʟʟαн(ﷻ)* Yana cewa:_
:
*"إن الله يأمركم أن تؤدوا الأمانات إلى أهلها"*
*_MA'ANA:_*
*_Lallai Aʟʟαн(ﷻ) Yanā umartarku da kumayar da amānōnī zuwaga ma'abotansu,_*
:
_Wāto da yawa wasu Mutānen sukan ɗauka cewa dukkan wani kāya indai na *Gwamnatine* to kawai abin banzane, wasu kuma sukan ruɗune da waɗansu *Shubhōhī* dan su halattawa kansu cin dukiyar *Al-Umma* ba bisa *ƙā'ida* ba, kamar Mutum yafake dacewa ai muma *Gwamnatin* tana zāluntarmu ko tana karɓar kuɗaɗe ahannunmu ba bisa *ƙā'ida* ba, danhaka bari muma mu *Sāci* kayanta sai mufanshe, to duk da haka bai halattaba Mutum ya *Sāci* dukiyar datake ta *Al-Ummace* gaba ɗaya yayi amfani da'ita ba bisa *ƙā'ida* ba, kuma koda kuwa *aƙarƙashin Gwamnatin Zāluncince ko ta Kāfirci,* haramunne yayi hakan, Sannan wasu kuma sukan ɗauka cewa ai dolene akan *Gwamnati* ta baiwa *Al-Ummarta Wutar-Lantarki da Ruwan-Famfo kyauta,* to idan hakane kenan sai ace kowa yadena fita *Kāsuwa* neman kuɗi, kawai yakwanta agida *Gwamnati* tariƙa ciyar dashi kyauta, duk dacewa inda *Gwamnati* zatace *Wutar-Lantarki da Ruwan-Famfo* kyautane batayi laifiba, hakanma akafiso tayi, saidai abin ya dangantane da *ƙarfin tattalin arziƙinta dakuma ādalcinta,* wanda wannan inma akwai *Ƙasāshen* da suke hakan to basu da yawa a *Duniya,*_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαппαп ʟıттαғı καмαя нακα:_*
*_↓↓↓_*
:
*"فتاوى اللجنة الدائمة" (23/441)*
:
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*Daga Zaυren*
*Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*_→AMSAWA←_*
*Mυѕтαρнα Uѕмαи*
*08032531505*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi