*_Tambaya ta (400)_*
:
_Menene hukuncin *Matar* da idan *Mijinta* yana saduwa da'ita saita suranta wani *Namijin* azuciyarta?? saboda gaskiya nidai *Mijina ƙazāmine* domin duk lokacin da zaizo kusa dani kawai sai naji ina *ƙyāmarsa,* danhaka idan yanemi yasudu dani nakan yardane kawai badon inasoba, wannan tasa duk lokacin dayake saduwa dani to nakan suranta wani *Namijinne* azuciyata ahaka har nagamsu, Shin Mālam menene hukuncin yinhakan a Muslunci??_
:
*Amsa:*
:
_*Mālamai sunyi Saɓāni* gameda hukuncin Mutumin da zairiƙa suranta wani azuciyarsa alokacin *Jimā'i* yaji kamar cewa tare dashine yakeyin wannan *Jimā'in,* Mazhabobin nan guda uku wāto:_
:
*_1-Hanābila,_*
*_2-Mālikiyya,_*
*_3-Hanafiyya,_*
:
_Duk sun tafine akan cewa harāmunne ga *Mace ko Namiji* ayāyin da suke sāduwar aure da juna Mutum yasuranta wani dabam acikin ransa, domin yin hakan sukace tamkar Mutum yana yin zinane da shi wanda aka suranta ɗin, Sannan *Mālamai* sukace kamar *Misālin* Mutum ne yaɗauki ruwa kokuma wani abinsha amma aransa sai ya suranta cewa *Giyāce* zai sha, sukace nantake wannan abin shan yā haramta agareshi yasha,_
:
_To ammā mafi yawā daga cikin *Mālaman* dake Mazhabin *Shāfi'iyya,* sun tafine akan cewa yin hakan yā halatta, daga cikin *Hujjarsu* akwai wannan Hadisi na *Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ)* da yake cewa:_
:
*"إن الله تجاوزلأمتي ما حدثت بها أنفسها مالم تعمل به أوتكلم"*
*_MA'ANA:_*
*_Aʟʟαн(ﷻ) Yā ɗaukewa al-ummāta laifin abinda zuciya tayi tunānin aikatāshi, matuƙar dai bai aikata abinba ko yayi furuci dashi:_*
:
_To Saidai kuma *Mālamai sunyi musu raddi* akancewa wannan Hadisin ba zai zama *Hujja* akan wannan aiki ba, domin kuwa shi wannan Hadisin yanā maganāne akan Mutumin da zuciyarsa zāta riyā masa yin wani abu maraskyau, kamar *Shan-Giyā, Sāta, Zina,* dadai sauransu, amma kuma baije yā'aikata wannan *Sāɓonba,* danhaka anyi masa afuwar wannan abinda zuciyarsa ta sāƙā masaɗin tunda bai aikatāba, to amma shi mai suranta wani aransa yayin jimā'i dāmā tunfarko da niyya yakāwo wannan tunanin don *yabiyāwā kansa buƙāta,* amma inda ace bai aikatāba to shikenan shimā hukuncinsa yāshiga cikin wancan Hadisi, danhaka *Mālamai* sukace maganar cewa yāhalatta ayi, wannan maganace mai raunin gaske,_
:
_Danhaka dai Maganā mafi inganci kamar yadda *Mālamai* suka faɗā itace: a *Shari'ance* bai halattaba ga *Namiji* lokacin dayake Jimā'i da *Mātarsa* ya suranta wata *Mātar* da ba tāsaba yaji kamar da itane yake jimā'i ahaka har *yabiyāwā kansa buƙāta,* wannan bai halattaba, Hakanan itama *Mace* bai halatta take suranta wani *Namiji* azuciyarta ba lokacinda *Mijinta* yake jima'i da ita,_
:
_Wannan kuma wata *Musībāce* da tayawaita tsakanin ma'aurata awannan zāmanin, zāka samu *Mace ko Miji* lokacinda sukeyin jima'i da junansu amma sai Mutum yasuranta wata Mace da yagani tabashi *Sha'awa,* ko Namijin da tagani yabāta *Sha'awa,* Shin azāhirine suka gani ko a *Film* kokuma ajikin *Hoto* dukkansu Harāmunne bai halattaba,_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
*_↓↓↓_*
:
*"الــمــدخــل" (2/195)*
:
*"ألآداب الشرعية" (1/98)*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*Daga Zaυren*
*Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*_→AMSAWA←_*
*Mυѕтαρнα Uѕмαи*
*08032531505*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi