MATSAYIN DIREBAN DA YAKE TUKA MOTA DA MUTANE SUKA MUTU

*_Tambaya ta (305)_*
:
_Meye hukuncin *DRIVER* n dayake tuka Mota sai yakade Mutum kokuma sukayi *ACCIDENT* wadansu daga cikin *PASSENGER* suka mutu??_
:
*_Amsa_*
:
_Dangane da magana akan hukuncin *Direban* da *yakaɗe Mutum* yamutu kokuma sukayi *haɗarin mota* akasamu asarar rayuka ko akaji ciwo, to dafarkodai za'akalli halayyar diraban ayayin dayake tuƙi, shin yanabin *ƙa'idar tuƙi* kokuma akwai sakacinsa aciki? *Aƙa'idar tuƙi* anabuƙatar dukkan wani direba yakasance yacika *ƙa'idar tuƙi* dakuma *Sharuɗɗansa,* sannan yana kiyaye dukkan wasu *dokoki dasuke da alaƙa da'ita Motar dakuma kiyaye dokokin da aka gindaya nakan hanya,* sannan yakasance yanada *ƙoshin lafiya* a lokacin dazaiyi *tuƙin,* yakasance *bayajin barci* kokuma *yagaji dayawa,* Sannan kafin *yatuƙa Motar* yakasance dama yayi *CHECKING* ɗin komai na *Motar* yaga  lafiya yake, kuma baya gudunda yawuce *ƙa'idar Motar* kokuma yanayin hanyar dayake tafiya akanta, kuma baiyi *OVERLOAD* amotarba, sannan kuma babu wata alama dayagani wacce takenuna masa cewa idan yaci gabada tafiya za'a'iya samun matsala,_
:
_To Idan yakasance dukkan wadancan *Sharuɗɗa* da aka ambata suncika, to a'irin wannan yanayi idan akasamu *haɗarin Mota* waɗansu suka mutu to babu komai akan wannan direban na biyan diyya kokuma yin kaffara, kamar yadda *ƙa'idar nan ta USUL takecewa*_
:
*"مالا يمكن التحرز عنه فلا ضمان فيه"*
:
_Danhaka kenan yazama wani *ibtila'ine* daga *Allah(ﷻ)* dayahukunta ya auku akansu kamar yadda *ibtila'in* na'iya faruwa akan kowa, domin shidai direba babu wani sakaci daga gareshi yabi dukkan wani sababi abisa *ƙa'idar tuƙi* kamar yadda yakamata abi,_
:
_Amma idan yakasance ansamu kishiyar waɗancan dokoki da *ƙa'idoji na tuƙi*, kamar yadda wasu direbobin babu ruwansu dabin wata dokar hanya ko *ƙa'idar tuƙi*, wanima yasan bashida cikakken birki amma ahaka *zaituƙa Mutane* wai sai ace ai *Aʟʟαн(ﷻ)* zaikare kuma sauka lafiya akebuƙata, hakikat *Aʟʟαн(ﷻ)* shine maikarewa to amma yasanyawa komai sababi, danhaka azahiri dole ayi aiki da waɗannan *asbab* ɗin da Ya ajje mana, amma sai *Mutum* yaƙi aiki dasu, to a'irin wannan yanayi idan akasamu *haɗari* yazama akwai sakaci kenan *taɓangaren direba,* danhaka hukuncinsa anan yayi kisane irin na kuskure danhaka dolene yayi kaffara ta hanyar yin *azumin watanni biyu ajere* akan kowanne Mutum guda ɗaya da yarasa ransa, sannan shi da danginsa zasu haɗu subiya *diyyar waɗanda suka mutu*, idankuma dangin mamatan sunyafe shikenan saidai yayi kaffara kaɗai, saboda faɗin *Aʟʟαн(ﷻ)*_
:
*"فمن لم يجد فصيام شهرين متتابعين توبة من الله……"  (سورة النساء..آية 92)*
_*MA'ANA:*_
*_(Allah yakecewa) wanda baisamu abinda zai 'yanta bawa ba to zaiyi azumin watanni biyu ajere yana mai tuba awajen Aʟʟαн(ﷻ)……,_*
:
_Danhaka kenan wajibine akan *Direbobi* suriƙabin dukkan *Sharuɗɗa* dakuma *dokokin tuƙi,* domin galibin *haɗuran* dasuke faruwa anan *Ƙasar* zakasamu akwai sakaci sosai ta ɓangaren wasu *direbobin*, *Aʟʟαн(ﷻ)* dai yakyauta:_
    *(وَالـلَّـهُ سُـبْـحَـانَـهُ=وَتـَعَــالـَيٰ أَعْـلَـمُ)*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιℓιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
                 *_↓↓↓_*
:
*"بدائع الصنائع" (7/273)*
:
*"التج والإكليل لمختصر خليل" (6/243)*
:
*"المغني...لإبن قدامة" (4/89)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
                       *(فِقْهُ الْعِبَادَاتِ)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
              *08032531505*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/

Post a Comment (0)