TARIHIN WALI DAN MARINA

TARIHI: WALI DAN MARINA
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Unguwar Masanawa a birnin katsina shahararriya ce koba komai saboda anan ne manyan Waliyai masu karamomi suka wanzu a karni na goma sha bakwai. Wadannan waliyai sune; Wali Dan Marina da kuma Wali Dan Masani.
Ance cikakken sunan wali Dan Marina shine Muhammad Ibn al-Sabbagh. Mahaifinsa balarabe ne wanda ya taso daga gabashi ya kuma sauka a katsina a gidan wani malami kuma attajirin Marini mai suna Kayaba. Wannan marini ance shine yake yiwa Sarkin Katsina na lokacin Mamuda da iyalinsa rinin tufafinsu.
Ana nan sai wata rana mahaifin wali dan marina yaga 'yar Sarki Mamudu wadda ake kira da baraka, yaji kuma ta kwanta masa. Don haka sai ya nemi aurenta, sai kuwa aka kuma aura masa ita akan sadaki zinare shidda. Suka tare a gidan kayaba. Bayan kimanin wata biyu sai Mallam Muhammadu mahaifin wali dan marina ya tashi izuwa gabas, ya bar baraka da cikin wali dan marina. Ita kuwa sai Allah yayi mata rasuwa kafin ta haihu, sai kuwa akaje aka binne ta a haka a kusa da wata bishiyar Marina.
Allah da ikonsa, sai ya Kadarta aka haifi Wali Dan Marina acikin kabarin nan na kusa da marina yana shan maman mahaifiyarsa a kabarin. Sai ya kasance yana fitowa lokaci lokaci yana yin wasa da dagwalon tukwanen baba, har wata rana mutane suka faki idonsa aka dauke shi riko wurin Wali Dan Masani, mai suna Mallam Abduljali.
Ance Wali dan Marina anan ya girma a inda ya nuna karamomi masu ban mamaki. A ciki akwai karamar karatun alkur'ani mai girma, inda ya kasance yana shan Kan malaminsa tun kafin a koya masa. Akwai kuma wata takaddama data tashi a gari game da watan azumin Ramadana, wasu suna cewa watan ya kare, sai aje a duba watan Sallah, wasu kuwa na cewa bai kare ba sai washegari.
To, da aka taru sai ba'aga wata ya tsaya ba. Sai Wali dan Marina ya fere fasasshiyar kwarya, yayi mata siffar wata, sannan ya jefa sama. Sai kuwa ta tsaya, ya nunawa mutane yace ga wata san. Sai kowa ya yarda wata ya tsaya.
To shikuma Wali Dan Masani sai ya musanta, yace wannan ba wata bane. Sai Yayi addua, ya mika hannu sama, sai gashi ya riko watan. Ya nunawa mutane, suka kuma yadda. Wannan itace takaddamar data shiga tsakanin waliyyai biyu, suka nunawa mutane karama.
Wali Dan Marina yayi rubuce-rubuce na littattafai da wakoki da dama. Misalin su shine:-
1. Wakar Daliyya wanda yayiwa Sarkin Berber Aliyu
2. Wakar Nuniyya wadda ta kunshi bayanin iliminsa
3. Wakar Toba mai baiti dubu
4. Kasidat Mazjarat al fiyan
5. Wakar yabon shehun Barno Mai Ali ibn Al Hajj Umar
Da wasunsu
(An ciro ne daga Kasidar da furofesa Dalhatu Muhammad ya taba rubutawa)

Post a Comment (0)