NAMIJI YA TSANI HAKA

🍃 *NAMIJI YA TSANI HAKA* 🍃


 🍃Idan har kina bukatar wani abu a hannun mijinki, to kar ki tambayeshi ta hanyar bashi Umarni da kuma nuna masa gadara kamar kice : " *Baban wane ! An aikomin da Ankon diyar su wane, inaso kabani kudin zan siya* ". Wannan sigar babu ladabi a cikinta, koda kuwa yana da zarafin siya din, sai kiga ya fasa, saboda kin biyo masa ta hanya Marar billewa. 

 🍃 Kamata yayi kibiyo masa ta hanyar neman Shawarar shi, kamar kice : " *Baban wane ! Ka ga su wance zasu aurar da diyarsu, kuma inaga ai kamar ya kamata nima nayi ankon nan , saboda yadda muke da su ko ?*

🍃 Insha Allahu sai ya fijin dadi da farin cikin bayani na biyun nan, kuma koda kuwa baiyi niyyar siya ba, amma sanadiyyar wannan sigar sai kiga ya siya miki. Lallaikam *maza ba sa son matansu surika basu umarni kamar su suka ajiye su*, sun tsani haka. 

*_Allah yasa mudace, kuma yakara kyautata tsakanin ma'auratanmu_*

✍🏻 *Idris M Rismawy*

2 Comments

Post a Comment