*WALIMA A MUSULUNCI*
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ
*TAMBAYA*❓
Asslm ya shaikh, tambayata: Shin walima nawa ce a musulunci? Kuma ya ake yinta asunnance?
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.
Shaikhul Mubajjal, wannan tambaya ce dake damun wasu musulmi saboda irin yadda aka riƙi walima da yanayin gudanar da ita.
Duk wanda ya karanta adabin Larabawa gabanin zuwan musulunci, zai ji cewa suna da kyawawan ɗabi'u da munana. Daga cikin kyawawan ɗabi'un su akwai tarar baƙo da ciyar da abinci ga mahajjatan jahiliyya da kuma marasa galihu, sun yi suna da hakan tun kafin zuwan musulunci.
Abu na biyu shine shari'a idan ta tara da al'ada, bata soke ta ko ta ƙyale ta, har sai ta auna ta a ma'aunin ta kafin ta haramta, ko ta mayar da ita addini ko ta halasta al'adar. Shi yasa a yau ma, yana cikin mafi girman ƙa'idojin usulul fiƙhi guda biyar, ita ce al'adatu almuhakkamah.
Duba da wannan shimfiɗar, akwai walimomi daban daban da Larabawa ke yi idan har dangantakar yin su sun taso, har wajen guda goma, ko sama da haka ma, kuma kowace na da sunan ta daban da na ƴar uwar ta. Ita walima gaiya ce ta cin abincin angunci kaɗai. Amma wasu Mallamai sun ce duk wani abincin da za'a gaiyaci mutane saboda wani abun farin ciki da ya faru, sunan shi walima. Da wannan gamammiyar ma'anar ce wasu suke kiran walima ko da freedom yayi ko ya iya karatun Suratul A'la ko izu biyar ko goma ko talatin ko sauka. Imamun Nawawiy yace ma'anar walima shine haɗawa ko tarawa, aljam'u, saboda haɗuwar ma'aurata guda biyu ake kiranta walima, hakan kuwa yace ya naƙalto ne daga Imamu Azzhuhuriy. Irin waɗannan Mallamai basu faɗaɗa ma'anar walima a aikace saboda rashin faɗaɗa ta a ma'ana. Amma Imam Ashshukaniy ya ƙulla hancin ma'anonin a wuri guda yace, ma'anar a yare, ta taƙaita a abincin angunci, amma kuma a shar'ance, duk wata haɗuwa da aka shar'anta walima ce.
Don haka sauran sun haɗa da
الوكيرة
Walimar sabon gida ko matsuguni idan Allah ya hore ma kamar yadda Hafiz yace. Amma Imamun Nawawiy da Ibnu Qudama sun ce walimar tarewa da miji
العذيرة
Walimar ɗan kaciya da ake idan ya warke ko an yanke shi.
العقيقة
Walimar sabon haihuwa rana ta bakwai da ake yi ko ranar suna kamar yadda muke kiran shi
الخرص أو الخرس
Walimar ranar da aka haihu ma'ana don nuna murnar mace ta haihu lafiya.
الشندخ
Walimar ƙulla auren don nuna murnar mallaka mallaka gabanin tarewa ko shiga ɗaki.
الحداق
التحفة
النقيعة
Abincin da ake ma matafiyi kafin ya iso don tarbar sa da nuna farin ciki da zuwan sa
الوضيمة
Abinci da ake shiryawa a kai ma wani saboda wata musiba da ta auka masa, kamar yadda Annabi yace a shirya abinci a kai wa iyalin gidan Jaafar haƙiƙa abin da zai shagaltar da ya zakke masu.
عن عبد الله بن جعفر قال : لما جاء نعي جعفر قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : اصنعوا لآل جعفر طعاماً فقد أتاهم ما يشغلهم ) رواه أهل السنن وصححه الألباني
النقرى
Abinci da za'a shirya saboda wasu mutane keɓantattu, ma'ana wane da wane. Irin ta ce Annabi yace mafi sharrin abinci, abincin walimar da aka hana wanda ya halarta ana kiran wanda bai zo ba
عن أبى هريرة أن النبي -صلى الله عليه وسلم- قال « شر الطعام طعام الوليمة يمنعها من يأتيها ويدعى إليها من يأباها ومن لم يجب الدعوة فقد عصى الله ورسوله ».رواه مسلم
الجفلى
Abinci da za'a shirya don mutane kowa ya zo yaci, ma'ana na ya ku bayi, kamar yadda Hausawa ke faɗi
المأدبة
Gaiyar cin abinci da abin sha ba tare da wani dalili ba, haka nan kawai.
العتيرة
Wannan wata walima ce ta Bid'ah da ake yanka akuya a raba, a ci, farkon watan rajab, bai halatta ba babu lada, Bid'ah ne.
Amma a taƙaice ga su kamar haka
الْأَطْعِمَة الْمُعْتَادَة الَّتِي تجْرِي مجْرى الشكران لها أَسمَاء مُتعَدِّدَة
1 _ فالقرى طَعَام الضيفان
2 _ والمأدبة طَعَام الدعْوَة
3 _ والتحفة طَعَام الزائر
4 _ والوليمة طَعَام الْعرس
5 _ والخرس طَعَام الْولادَة
6 _ والعقيقة الذّبْح عَنهُ يَوْم حلق رَأسه فِي السَّابِع
7 _ والغديرة طَعَام الْخِتَان
8 _ والوضيمة طَعَام المأتم
9 _ والنقيعة طَعَام القادم من سَفَره
10 _ والوكيرة طَعَام الْفَرَاغ من الْبناء
تحفة المودود لابن القيم
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakara Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*
ASSALAMUALAIKUM WARAHMATULLAH ALHAMDU LIL-LAH ALHAMDU LIL-LAH ALHAMDU LIL-LAH, MUNAGODEWA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, KUMA MALAN MUNA NEMAN KUYIMANA WATA SOFTWARE MAISUNA { WALIMA A MUSULUNCI } WADDA ZATA QUNSHI MA'ANAR KALMAR WALIMA DA BAYANAI MASU MUHIMMANCHI IDAN ALLAH YABADA IKO, MUNAFATAN ALLAH YABADA IKON YIN WANNAN SOFTWARE MAI MUHIMMANCHI KUMA DA YARENMU NA HAUSA ALLAHUMMA TAQABBAL MINNA WAMINKUM AMEEN.
ReplyDeleteAmin, Allah ya bamu iko. Jazakallah Khair
DeleteMASHA ALLAH ALLAH HISAKA KUMA ALLAH YASA MANA ALKHAIRI DA AL-BARAKAH AMEEEEN.
ReplyDelete