*_Tambaya ta (429)_*
:
_Shin ko ya halatta ga *Mace* idan mai nemanta da aure yaje wajenta, tazo wajensa ba tare da ta sanya *Hijabi* ba??_
:
*Amsa:*
:
_Asalidai *Shari'a* ta Umarci *Maza* da *Mātā* cewa su rintse idānunsu ga barin yiwa junansu kallo irin na *Sha'awa,* kamar yadda *Aʟʟāн(ﷻ)* yafada:_
:
*قل للمؤمنين يغضوا من أبصارهم ويحفظوا فروجهم ذالك أزكي لهم………إلخ*
*_MA'ANA:_*
*_(Yā Muhammad(ﷺ) kagayawa Muminai (Maza) su rintse idānunsu kuma sukiyaye Farjinsu, hakan shine yafi tsarkaka agaresu………_*
:
_To amma *Shari'a* tayi izini ga mai neman aure yakalli *Mātar* da yakeso ya aura, to Saidai kuma *Mālamai* sunyi *Saɓani* dangane dacewa inane iyakar *gwar-gwadon* inda yakamata Maneminta yakalla ajikinta? Wasu daga cikin *Mālamai* sai suka tsananta dayawa sukace bai halatta aga komai ajikintaba, Wasu *Mālaman* kuma sai suka *Sassauta* dayawa, sukace ya halatta yaga komai ajikinta in banda tsiraicinta *kaɗai,* daga cikin Hujjarsu akwai wannan Hadīsi na *Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ)* da yake cewa:_
:
*''إذاخطب أحدكم المرأة فإن استطاع أن ينظر إلي ما يدعوه إلي نكاحها فليفعل''*
*_MA'ANA:_*
*_Idan Ɗayanku yana neman Mace da aure, to idan yasamu ikon yakalli abinda zaija hankalinsa ya aureta, to ya'aikata (yakalla):_*
:
_Sannan kuma akwai *Mālaman* da suka tsaya atsakiya, wato basu tsananta da yawaba kuma basu Sassauta dayawaba, wanda ko *Shakka bābu* cewa mafi yawa daga cikin *Mālamai* duk sun tafine akan wannan ra'ayi na *Tsaka-Tsakiya,* daga cikin Hujjarsu akwai wannan āya da *Aʟʟāн(ﷻ)* Yake cewa:_
:
*''ولا يبدين زينتهن إلا ما ظهر منها''*
*_MA'ANA:_*
*_Kada Mātā su bayyana adonsu saidai abinda yake bayyananne daga ciki (Fuska da tāfin Hannu):_*
:
_Danhaka *Mālaman* dake Mazhabobin *Mālikiyya, Shāfi'iyya,* dakuma *Hanafiyya,* sukace iyākar *Fuska* da *Tāfukan-Hannu* kaɗai ya halatta yagani, sukuma Mazhabin *Hanābila* sukace ya halatta manemin aure yakalli dukkan gurinda abisaga al'āda yakan iya bayyan aganshi ajikinta, Musamman irin wuraren da kan bayyana ajikin *Mace* yayin da take cikin gida tanayin wasu *'Yan aikace-aikace* irin na cikin gida, wāto kamar *Wuyanta,* *Hannāyenta,* *Ƙafāfuwanta,* dakuma *Gāshin kanta.*_
:
_To amma Maganar datafi *inganci kuma tafi dalilai masu Ƙarfi* kamar yadda mafi yawan *Mālamai* suka rinjayar itace, ya halatta mai neman aure yakalli *Fuskarta,* da *Tāfukan-Hannayenta* da *Wuyanta,* da *Duga-Duganta*, dakuma *Gashin kanta* in buƙātar Hakan takama, saidai wasu *Mālaman* sukace idan yakalla sau ɗaya to shikenan ya wadatar, daga nan kuma bai halatta yasake kalloba, amma wasu *Mālamam* sukace ya halatta yamai-maita kallonta idan *buƙatar hakan takama,* koda kuwa ba tareda tasan yana kallonta ɗinba, saidai bai halatta yayi mata kallo irin na *Sha'awaba* wanda zai sashi yaji dāɗi aransa, Sannan wannan hukuncin yana tabbatuwane akan Mutumin da yazo neman aure tsakaninsa da *Aʟʟāн(ﷻ)* dagaske yakeyi bawai dawasa ko yaudara yake yiba, sannan yanada tabbas kokuma zato mai rinjaye akan cewa idan yanema za'a karɓeshi ayarda da dashi, Sannan da sharaɗin ya kasance babu wani wanda yake nemanta da suka amince dashi, saboda *Mαnzon Aʟʟāн(ﷺ)* yahana wani yanemi aure akan neman wani:_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*_※AMSAWA※_*
*Mυѕтαρнα Uѕмαn*
*08032531505*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
:
*_Doмiп пεмαп ƙαrıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαr нακα:_*
*_↓↓↓_*
:
*"بدائع الصنائع" (5/122)*
:
*"المغني لإبن قدامة" (7/453)*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
*Daga Zaυren*
*Fiƙнul-Iвādāт*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє Fαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi