_*Tambaya:*_
Assalamu alaikum malam dan allah inaso ayi min bayanin yadda ake wankan haila nagode.
_*Amsa*_
_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._
_Wankan haila, da na janaba da na biki da sauransu duk daya ne, babu wani bambanci sai a Niyya._
_Ga siffar Wankan janaba nan kamar yadda ya zo a hadisin Ummuna Aisha (r.a):_
_An karbo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce: ((Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan zai yi wanka na janaba, yana farawa da wanke hannayensa, sannan sai ya zuba ruwa da damansa a bisa hagunsa, sai ya wanke farjinsa, sannan ya yi alwala. Sannan ya kama ruwa sai ya shigar da yatsunsa a cikin asalin gashin kanshi, sai ya zuba ruwa a kanshi sau uku, sai ya game jikinsa da ruwa, sannan ya wanke kafafunshi)). Bukhary da Muslim, lafazin Muslim ne._
_A takaici wannan hadisin na koyarda mu yadda ake yin wankan tsarki ne, imma (janaba, haila, biki, Wankan Juma'a da sauransu)._
_'Yar uwa idan kin tashi za ki fara ne da wanke hannayenki, sannan ki yi tsarki da hannun hagu tare da wanke duk inda najasa ta ta6a, sannan sai ki yi alwala kamar yadda kika saba yi idan za ki yi sallah, sannan sai ki wanke gashin kanki tare da cuccudawa, ki sanya yatsunki har zuwa kasan gashin sau uku, sannan sai ki game jikinki da ruwa._
_Babbar manufar dai shi ne ya kasance ruwa ya isa kowani lungu da sako na jiki, don haka duk inda aka ga ruwa be isa ba, sai a isar da shi._
_Wallahu a'lamu._
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_