*ZAN IYA RARRABA KAFFARAR RANTSUWA ?*
*Tambaya:*
Aslm.Dr. don Allah a amsa mana wannan tambayar. Ya halatta in raba kaffarar azumin rantsuwa?
*Amsa*:
Wa alaikum assalam, ya halatta a rarraba azumin kaffarar rantsuwa, saboda aya ta: 89 a suratul Ma'ida da ta yi bayanin kaffarar rantsuwa ba ta kayyade azumi ukun da jerantawa ba, wannan yasa da yawa daga malamai suka tafi akan halaccin rarraba azumin.
Ba'a yin azumi uku a kaffarar rantsuwa sai ga wanda ya kasa ciyar da miskinai goma ko tufatar da su, kamar yadda ayar ta yi bayani dalla-dalla akan haka. Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
26/05/2016