*_MUTUM YANA DA HALAYE GUDA UKU:_*
*_1- Imma ya zama in ya san gaskiya zai yi aiki da ita._*
*_2- Ko in ya san gaskiyar ba zai yi aiki da ita ba._*
*_3- Ko kuma in ya san gaskiyar zai yi musu da inkarinta._*
.
.
.
1. To na farko a cikin wadannan shi ne wanda za a yi masa Da'awa ta hanyar bayani na hikima, wato ta hanyar bayanin Ilimi da aiki da shi.
2. Na biyu kuma shi ne wanda za a yi masa Da'awa ta hanyar wa'azi, wato a kwadaitar da shi rahamar Allah a tsoratar da shi azabarsa, don ya yi aiki da gaskiyar da ya sani.
3. Amma na uku kuma shi ba Da'awa ake yi masa ba, Jidali ake yi masa bisa niyyar tsare mabarnaci ga Addini. Don haka duk wanda ya yi inkarin gaskiya bayan ya santa to za a yi masa Jidali ne ta hanya mafi kyau don ayi maganin taurin kansa da jayayyar da yake yi a kan karya.
Allah ya ce:
{ﺍﺩْﻉُ ﺇِﻟَﻰ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺭَﺑِّﻚَ ﺑِﺎﻟْﺤِﻜْﻤَﺔِ ﻭَﺍﻟْﻤَﻮْﻋِﻈَﺔِ ﺍﻟْﺤَﺴَﻨَﺔِ ﻭَﺟَﺎﺩِﻟْﻬُﻢْ ﺑِﺎﻟَّﺘِﻲ ﻫِﻲَ ﺃَﺣْﺴَﻦُ ﺇِﻥَّ ﺭَﺑَّﻚَ ﻫُﻮَ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﻤَﻦْ ﺿَﻞَّ ﻋَﻦْ ﺳَﺒِﻴﻠِﻪِ ﻭَﻫُﻮَ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﺎﻟْﻤُﻬْﺘَﺪِﻳﻦَ} [ ﺍﻟﻨﺤﻞ : 125 ]
Amma shi ma Jidali ta hanya mafi kyau din dole ya kasance da ilimi kamar yadda bayani da hikima ma da ilimi ake yinsa.
{ﻫَﺎﺃَﻧْﺘُﻢْ ﻫَﺆُﻟَﺎﺀِ ﺣَﺎﺟَﺠْﺘُﻢْ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻟَﻜُﻢْ ﺑِﻪِ ﻋِﻠْﻢٌ ﻓَﻠِﻢَ ﺗُﺤَﺎﺟُّﻮﻥَ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻟَﻴْﺲَ ﻟَﻜُﻢْ ﺑِﻪِ ﻋِﻠْﻢٌ} [ ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ : 66 ]
Saboda haka Allah bai yi umurni da ka yi Jidali wa mai taurin kai da jahilci ba, ko da hujjojin da ba zai mika wuya gare su ba. Shi ya sa ba a raddin bata da wata batan, sai dai in za ka yi amfani da ita ne don ka bayyana bacin ra'ayin nasa da bayyana tufka da warwaransa, amma ba don ka tabbatar da gaskiya da kira gare ta da batan ba. Duk da cewa; Manhajin Al- Qur'ani shi ne bayanin gaskiya da kira zuwa gare ta.
Saboda haka, ya kamata Malamai da Daliban Ilimi masu Da'awa da Mujadala wa masu taurin kai ma gaskiya su lura da wannan babi.
Daga:- Dr. Aliyu Muh'd Sani
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.