*_ALLAH BAI KAYYADE LOKACIN RAMA AZUMI BA !!!_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum, Dr. Mace ce ta sha Azumin shekara uku ajere saboda ciwon ulcer, kuma abin da zasu kai baki gagaransu yake ballatana ta ciyar. Menene mafita?
*Amsa*
Wa'alaikum assalam Ta jira har Allah ya bata lafiya sai ta rama.
Allah madaukakin sarki a cikin Suratul Bakara aya ta: (185) ya sanya ramuwar azumi ga mara lafiya a wasu kwanaki na daban don ya nuna abin a bude yake, zuwa lokacin da aka samu dama, ba tare da yin sakaci ba.
Allah ne mafi sani.
03/03/2018
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.