Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Gareku masoyana,don Allah,don Annabi,duk inda kukaga anzageni,karku ramamin,kubar mutum,da halin shi,kamar yadda kuka saba bani haɗin kai kuci gaba na in kunga sakon zagin kubarshi can inda kuka gano shi,karku damu da zagin nasu kamar yadda nima be dameniba,Sabida abun kunyane ga zaki ya tsaya musayar yawu da ɓera,surbajo ce#haka nake,atare abuge ba dama,abari in wuce ga haushi,Allah kaimin komai har Abada Alhamdulilahi*
*5*
Cike da farinciki salma takoma camp,tun a hanya ta tsaya ta sayi duk abinda bata dashi sannan ta ƙarasa.
Feefee tayi mamakin ganin salma da kudi wanda tasan bata dasu,dan haka tambayarta tayi.
"Salma ina kika samo kudi haka?"
Dariya tayi sannan tace.
"Tsinta nayi a gurin aykinmu"
"wacce irin tsuntuwace wannan,ta kuɗi me yawa,kuma waya faɗamiki,in ka cinci kuɗi ya zama naka ,ko cigiya nasan bakiyiba haba salma abun da kikeyifa be dace ba"
"To uwar ile,nide na tsinta kuma nakashe,karki dameni kuma,ke komai mutum yayi idonki nakai,pls kiɗan rage sa ido don Allah mtssuu"
Feefee bata sake magana ba,illah zuba mata ido da tayi.
Washe gari da asussuba salma ta shirya,ƙarfe shida tanufi gurin ayki,acan bakwai taimata.
A ɓangaransu ta riga kowa zuwa,dan haka office ta shige tayi zamanta.
Bata jimaba tafara jiyo hayaniyar mutane a waje,tana nan zaune marry ta shigo.
"Ah salma kene da sassafe haka kamar wacce ta kwana anan?"
Tsaki salma tayi sannan tace.
"Wannan ɗan balain ne yace kar in bari bakwai tayi banzo gurin Aykiba,shiyasa kika ganni anan da wuri"ta ƙarasa maganar cikin yanayin damuwa.
Dariya marry takeyi harda tuntsurawa sannan tace.
" kin faɗa tarkon doctor,kita addua Allah ya rabaku lfy,dan bashi da daɗin shaani sam".
Shuru salma tayi kawai tan nazari a zuciyarta.
Doctor Najeeb se ƙarfe takwas ya iso asibitin kai tsaye office ɗinshi ya shige,yana zama,ya kunna computer dake haɗe da cct camara,dan ganin abinda ya wakana kamin yazo,
Ba ƙaramin mamaki yayiba sanda ya hangi salma tana kwashe kuɗin daya bari akan table jiya,wanda shi inbanda yanzu daya gani yama manta da kuɗin,sosai yayi mamaki,aranshi yace.
"she is so beautifull,but ba hali me kyau,iwill make sure that i play with her intelligent"yayi want keeler smile ta gefen bakinshi.
Jin doctor yazone yasa salma miƙewa tanufi office ɗinnashi,sallama tayi baa jimaba ya amsa yabata izinin shiga.
Tana shiga taga ya ƙureta da ido,har tsarguwa tayi ta kama ƴan soshe soshe alamun rashin gaskiya.
"have a sit".
taji yace,jiki a sanyaye tazauna,ta gaisheshi ya amsa.
Daga haka bece mata komaiba yafara duba marasa lafiya,wainda suke matane,kasancewarshi, doctor,wasu tambayoyin in yana yiwa patient ɗin har kunya suke ba salma shiko ko ajikinshi,itade tana sauraronsu tana jorting a littafinta na abinda take ganin bazata iya riƙewaba.
be dakatar da duba marasa lafiyanba,se da azahar,dan haka miƙewa yayi yacire agogonshi yashiga toilet yayi alwala ya wuce masallaci,yana sane yayi kamar yamanta da ogogon,wanda kuɗinshi yafi dubu ɗari.
Yana fita salma ta ƙarasa haɗa Takardun gurin ta adana,har ta miƙe zata fita itama,se idonta ya sauka kan agogon,tsayawa tayi tana kallonshi,tana tunanin ɗauka,tana jin tsoro.
Ƙarasawa tayi gurin agogon,sede abinda ta hanga aƙasan table ɗin yafi mata agogon,amfani,kuɗine bunch bunch na one thousands guda huɗu.
jiki na ɓari tasa hannu ta ɗauki ɗauri ɗaya,harta tafi sekuma ta sake dawowa ta ɗauki ɗaya yazama dubu ɗari biyu kenan,cikin aljihunta ta zuba kuɗin,tafice daga office ɗin da sauri.
Jakarta taje ta zuba kuɗin aciki sannan tayi sallah,ta koma office ɗin doctor tana ta adduar Allah de yasa be duba kuɗinshiba.
Shiko doctor duk yana sane ya ajiye kuɗin dan yagani iya ƙananan sata ta iya koko harda manya ma,ilai kuwa koda yadawo daga masallaci,dubawa yayi yaga babu dan haka kunna computer yayi dan yaga yadda abun yafaru.
Sosai yasha mamaki,daga ƙarshe abun yabashi dariya,ba abinda yafi bashi dariya kamar yadda ta ɗauki na farko har ta tafi taga be ishetaba ta dawo ta ƙara na biyu.
Kashe computer yayi yashiga tunanin ta ina ze ɓullowa wannan me hannun ɓeran da aka haɗashi ayki da ita.
Sallamar salmace ta dawo dashi daga duniyar tunanin,izinin shigowa yabata.
Tana shiga yamiƙe afusace,yace.
"uban waye ya dau..."bata jira yagamaba jikinta narawa bakinta na karkarwa tace.
"wallahi doctor ban ɗaukar maka kuɗiba"
Dariyace taso kamashi,ganin yanayin da salma tashiga,dakewa yayi yasake dakamata tsawa yace.
"kinji nace miki,an ɗaukemin kuɗine?baki jira nagama maganaba kin katseni,to cewa zanyi waya ɗauke takardun danake ayki akansu".
Wata uwar ajiyar zuciya salma tasaki harda dafe ƙirji ta jingina da bango ta lumshe ido na ƴan mintuna.
Dariyace sosai cike da cikin doctor amman se yadanne.
Salma baki na rawa gumi na keto mata tace.
"nice na kwashe na zuba maka a loka,bari in ɗauko,maka"kamar mazari tanufi lokar ta ɗauko takardun ta bashi,suka ci gaba da duba patients,lokaci zuwa lokaci doctor na lura da yadda salma take ta faman sakin ajiyar zuciya.
haka sukai ta duba marasa lafiyan har zuwa sanda sukayi changen duty.
Jiki na ɓari salma tafice daga Asibitin,aƙafa take tafiya,dan gaba ɗaya a rikice take tama kasa tsaida mashine ta hau,dan tunda take sata bata taɓa yin babba kamar wannan ba.
Motar doctor taga yasha gabanta kaɗan yarage ta saki fitsari a wando,sabida tsoratar datayi,kasa ci gaba tayi da tafiyar,shiko duk yanayin data shiga yana observing, da ƙyar ta ƙaraso inda yake taɗan rusuna ta gaisheshi.
"shigo in rage miki hanya"doctor yace batare daya kalletaba.
Da cewa zatayi ta gode,sekuma taji tsoron kar rsnshi ya ɓaci wataƙila ma yagano,ita ta ɗaukarmasa kuɗi ya tozartata a gurin,danhaka ba musu tashiga motar suka tafi.
Se ƙara rungume jakar ta takeyi takasa sakinta.
"Hala de jakarnan taki akwai wani abu me muhimmanci acikine ko?"doctor ya wurga mata tambaya.
A kiɗime ta waigo tana kallonshi tace bakinta na rawa.
"Aa wlh ba kuɗi bane acikiba"ta bashi amsa tana ƙara riƙe jakar da kyau.
"ke ko kode kunnenki beji dakyaune a ina kikaji na ambaci kuɗi?".
Jan bakinta tayi tai shuru,har suka iso camp ɗin yasauketa,har ta sauka daga motar,se ya leƙo da kanshi ta window yace.
"To akashe lafiya".
yana faɗin hakan,yaja motarshi ya barta agurin tana nazarin kalmarshi.
"akashe lafiya,to me yake nufi kenan?"salma ta tambayi kanta,rashin amsane yasa ta juya tawuce ɗakinsu.
surbajo ce,for life.