BABBAR MAGANA

🤣🤣🤣🤣😄😄Wata matace ta shiga dakin mijinta wanda yasha gyara tace mishi "baban Salim gaskiya ya kamata kayi kokari ka halarci wannan daurin auren na aminiyata. Sai yayi dariya yace ai zuwa daurin auren aminiyarki ya zama dole, yanzu me zaki kai mata gudummawa? Tace kudine dubu biyar, sai yace gaskiya biyar yayi kadan, ga goma ki kara.Ta karba ta mai godiya ta shirya ta tafi. Da aka gama biki kowa yayi haramar raka amarya gidanta, maman Salim ce babbar kawa ta kame a kusa da amarya. Abu kamar wasa taga an miki hanyar unguwarsu, sai tace ashema muna kusa, amaryar tace ai kusa sosaima. Bata ankara ba taga anyi parking a kofar gidansu, sai kuwa kowa ya fito, ta dubi direban tace malam ba nanne gidan ba, wannan gidanane. Nan fa musu ya hargitse, kwatsam sai ga miji (baban salim) da abokanshi, yana zuwa beyi wata wata ba sai ya rungume amaryarshi (watau amaryar da aka kawo) ya shige da ita gidan har cikin dakinshi. Too yanzu lnkece yazakiyi 🤣🤣🤣😄😄😱😱

Post a Comment (0)