CINIKIN ƘARA RIBA

*بيع المرابحة*
*CINIKIN KARA RIBA*
      *TAMBAYA*
❓❓❓❓❓❓❓❓
Assalamu alaikum
Warahmatullahi
Mallam mutunne ya bude  ma wani  shago na aski, sai yace masa duk sati ko wata ga abin da zai dinga bashi acikin abin da yake samu,  shi kuma yaron sai yace a'a saidai ayi lissafin abin da aka kashe gaba daya a shagon sai ya Kara ma maigidan wani abu akai Sannan duk wata sai ya dunga ragewa har ya gama biya.shin yaya matsayin wannan Kari da zaiyi

    *AMSA✍*
Wa alaikumus salamu warahmatullah.

👉(1). Idan ya saya kuma ya fadi gaskiyar abinda ya saya, Sai aka kara masa riban babu laifi,
Wannan shi ake kira *BAI'UL MURAABAHA, cinikin kara Riba,* inya biya yadda aka tsara yayi babu laifi.
Akwai bayanin acikin iziyyah.

👉(2).
🇦. Amma idan ya sayi abu misali dubu biyar sai yace: dubu shida yasayeshi, to yayi karya kuma wannan dubu daya da yakara ta zama Haramun, kuma ga abinda za'akara masa.
Annabi Sallallahu alaihi wa sallam yace:(MASU CINIKI DUKA SU BIYUN SUNA DA ZABI,
IDAN SUKAYI GASKIYA KUMA SUKA BAYYANA AIBIN GASKIYAR KAYAN, SAI AYIMASU ALBARKA ACIKIN CINIKINSU,
IDAN KUMA SUKAYI KARYA KUMA SUKA BOYE AIBI, SAI ASHARE ALBARKAR CINIKINSU). Buhari:2112. Mislim:1531.

🇧. Sa'annan idan ana sayansa asari 5000, asaida 7000, Amma sai yace: tunda ahankali zai biya, to za'akara masa 3000, domin tsagwan tsagwan zai biya,
Wannan shi ake kira *Albai'u Bittaqsit,* akarawa kayan saidawa kudi domin za'abiya tsagwan tsagwan, shima Haramunne.

🇨. Sannan idan akace kudi hannu 5000, Amma bashi 7000, to haramunne, domin kuwa ba'atabbatar ma kayan kudi daya ba,
Shine ciniki biyu cikin ciniki daya da hadisi yazo dashi kuma yahana.
📓 Jami'i:6943.
*Mai Askari yayi bayanin hakan.*

*=================*
Wallahu ta ala a alam.
*Shafi'u ShehuMinna.*
Daga Islamic Group.

Post a Comment (0)