DIMOKURAƊIYYA: ƳANCI GA KUDU AZABA GA ƳAN AREWA

Copied
Nafeesa Shuaibu ta rubuta:

DIMOKRADIYYA: 'Yanci Ga 'Yan Kudu Azaba Ga 'Yan Arewa

Cikin ruwan sanyi Bola Ahmed Tinibu ya kalli Gwamnan jihar Legas ya ce ba ma sonka, salin-alim ya ce to na hakura. Amma jihar Zamfara an yi kone-kone, an yi Zanga-zangar Korar Yari, an rasa rayukan TALAKAWAN jihar, amma Gwamna Yari da ake kira SHEHI ya ce komai zai faru ya faru.

Jihar Kano da ta fi yawan Al'umma a Najeriya, cibiyar Musulunci da Kasuwanci ana ta rigima tsakanin tsohon Gwamna da Sabon Gwamna kusan Shekaru uku, babu wanda zai iya sulhuntawa. An raba kan Al'umma, an yarjewa talakawa daukar makami gami da gaba da juna akan bukatun mutum biyu kacal.

Idan abu ya faru a Kudu cikin ta gaggawa fadar Shugaban Kasa za ta fitar da sanarwa na Allah Wadai gami da magana da kakkausar murya cewa a gaggauta daukar mataki. Amma idan a Arewa ne sai an bi a sannu ana fadin bin doka da oda, saboda tsoron kada a danganta shi da mai son yankinsa.

Yobe an mayar da ita kamar wasu tsirarun mutane aka haifawa ita sai yadda suka dama haka kowa zai sha.

Mataimakin Shugaban Kasa Kirista ne mamallakin babban coci, wanda ya ke da ikon yin addinin sa yadda ya so, amma Musulmin Shugaban Kasa tsoro ya ke ji kada a danganta shi da mai tsattsauran addini.

Da zarar an taba 'yan Kudu a Arewa sai Kafafen Sadarwa su yi caa, amma idan 'yan Arewa ne sai ka ji shiru. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama su yi ta babatu, manyan sojojin su su yi ta Kumfar baki, amma idan aka taba Dan Arewa wanda a can, SHIRU ba komai.

An samu kududdufin kisa a kashe a jefa har da babban Soja, amma shiru ka ke ji kowa ya tafi neman kuri'a.

Kungiyar Kiristocin Najeriya sun iya fitowa su yi wa Shugaban Kasa barazana akan mabiyan su, amma mu namu kungiyoyin addinin sai fada da juna.

Manyan jagororin siyasar mu na can suna Zanga-zangar murdiyar zabe, amma sun kasa cewa uffan akan murde wuyan 'yan Arewa.
Fasto na da 'Yancin Fadin abinda ya ga dama amma Malami tsoro ya ke kada a kira shi Dan TA'ADDA.

Manyan 'yan Bokonsu na da 'yancin rubuta duk abinda suka so akan mu, amma mu namu sai dai son Gwanintar iya Turanci.

A yi ta nuna manyan ayyukan raya kasa a Kudu, mu kuma Arewa sai hotunan Gawa da na Matasan mu dauke da makami a tarukan siyasa.

Post a Comment (0)