ADADIN SHARUƊƊAN SALLAH DA SUKE ZAMA SABABIN KARBAR SALLAR MUTUM
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
*TAMBAYA*❓
Assalamu alaikum.
Allah shi qara wa mallam ilimi da taqawa, Dan Allah ga tambaya ta Sharuddan karban Sallah tare da nassin Hadith ko Ayan Qur'an.
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah.
Ko shakka babu Malamai sun baiyana cewa sallah na da rukunnai, wajibai da mustahabbai. Sun kuma nuna cewa duk sallar da ta rasa rukuni ɗaya daga cikin rukunnan ta, babu wannan sallah, sai dai a sake ta.
Amma idan aka rasa wajibi ana iya gyara ta, a inda idan mustahabbi aka rasa ko ba'a zo da shi ba, sallah ta yi.
Kafin mu ambaci rukunnan sallah kamar yadda ka bukata, yana da kyau mu tantance tsakanin sallah ta yi, da kuma an karɓi sallah. Ababe ne biyu mabanbanta juna, da farko dai ana iya gane cewa sallah ta yi, ko ta inganta, don al'amari ne na zahiri da ido, zai iya gani saɓanin ace an karɓi sallah, wannan babu yadda za'a iya sanin haka, domin al'amari ne ɓoyayye, na gaibi, da Allah kaɗai ya bar ma kan Shi sani. Na biyu sallah na iya zamowa ta yi, amma ba'a karɓa ba, domin ita karɓa da rashin karɓa ganin dama ne na Allah da ya dace da ilmi da hikima ta Shi Subhanahu wa ta'ala.
Don haka, abin da yafi muhimmanci, bayan mutum ya zo da rukunnan sallah kamar yadda ya karanta, toh sai ya bi ta da tawali'u da zargin kan shi da tsoro da fatan a karɓa, kamar yadda Allah yace dangane da mutanen kirki da suka san matsayi da girman Allah
(وَٱلَّذِینَ یُؤۡتُونَ مَاۤ ءَاتَوا۟ وَّقُلُوبُهُمۡ وَجِلَةٌ أَنَّهُمۡ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ رَ ٰجِعُونَ)
[Surah Al-Mu'minun 60]
Hadisin Nana Aisha ya fassara mana ayar inda ta tambayi Annabi, sune mazinata, mashaya giya? Yace da ita, a'a, ƴar Siddiq, wanda suka yi sallah suka bayar da zakka ne, tare da haka zukatan su na cike da tsoro, Allah ya karɓa ko bai karɓa ba.
سألت عائشة رضي الله عنها عن هذه الآية فقالت: يا رسول الله أهو الذي يزني ويسرق ويشرب الخمر قال: لا يا بنت أبي بكر أو يابنت الصديق، ولكنه الرجل يصوم ويتصدق ويصلي وهو يخاف أن لا يتقبل منه الله . رواه أحمد والترمذي وابن ماجه، وهذا لفظ ابن ماجه، وصححه الألباني وغيره.
A yau galibi mun rasa jin irin haka a jikin mu, da zaran mutum ya gabatar da wata ibadah, sai ka ji shi yana cewa, an karɓi wannan, ko kuma wannan ta wuce sai dai wata, idan kuma har bai buɗe baki ya faɗi hakan ba, a ran shi, ko a zuciyar shi, yana nan yana kallon sauran mutane, kallon ƴan wuta ne ko halakakku, shi kam ya haye, jira yake a busa ƙaho kawai ya shige aljanna, har ma idan ana wani wa'azi yana jin da su wane ake, ba da shi ake ba, shi da ya haddace alqur'ani, yake zuwa makaranta, yake kaza da kaza da kaza, subhanallah, Ɗan uwa, abun ba haka yake ba, yanzu ka fara kuma ba kayi komai ba, nan kusa idan ka koma tarihin magabata, zaka ramma kan ka.
Zan baka amsa amma ban yi maka alƙawalin komai sai na baka aya ko hadisi ba kamar yadda ka sharɗan ta min, sai ka je ka binciki littafai don samun ayoyin da hadisan, a nan kusa, akwai littafi mai suna
١) الفقه على ضوء الكتاب والسنة
٢) صحيح فقه سنة
Insha Allahu zaka samu dalilai rututu daga alqur'ani da Hadisai.
Rukunnan sallah ga su kamar haka, idan na manta wani sai kayi min afuwa
1)Ikhlasi
(وَمَاۤ أُمِرُوۤا۟ إِلَّا لِیَعۡبُدُوا۟ ٱللَّهَ مُخۡلِصِینَ لَهُ ٱلدِّینَ حُنَفَاۤءَ وَیُقِیمُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَیُؤۡتُوا۟ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَ ٰلِكَ دِینُ ٱلۡقَیِّمَةِ)
[Surah Al-Bayyinah 5]
2)Niyya
((إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ وَإِنَّمَا لِكُلِّ امْرِئٍ مَا نَوَى.... )).
(وَمَنۡ أَرَادَ ٱلۡـَٔاخِرَةَ وَسَعَىٰ لَهَا سَعۡیَهَا وَهُوَ مُؤۡمِنࣱ فَأُو۟لَـٰۤىِٕكَ كَانَ سَعۡیُهُم مَّشۡكُورࣰا)
[Surah Al-Isra' 19]
3)Musulunci
(وَمَن یَبۡتَغِ غَیۡرَ ٱلۡإِسۡلَـٰمِ دِینࣰا فَلَن یُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِی ٱلۡـَٔاخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَـٰسِرِینَ)
[Surah Aal-E-Imran 85]
4)Hankali
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((رُفِعَ الْقَلَمُ عَنْ ثَلاَثَةٍ عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ وَعَنِ الْمُبْتَلَى حَتَّى يَبْرَأَ وَعَنِ الصَّبِيِّ حَتَّى يَكْبَرَ)).
5)Shigar lokaci
(.... إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِینَ كِتَـٰبࣰا مَّوۡقُوتࣰا)
[Surah An-Nisa' 103]
6)Tamyizi ko Girma (shekarau goma da haihuwa)
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((رُفِعَ الْقَلَمُ عَنْ ثَلاَثَةٍ عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ وَعَنِ الْمُبْتَلَى حَتَّى يَبْرَأَ وَعَنِ الصَّبِيِّ حَتَّى يَكْبَرَ)).
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((مُرُوا أَوْلاَدَكُمْ بِالصَّلاَةِ وَهُمْ أَبْنَاءُ سَبْعِ سِنِينَ وَاضْرِبُوهُمْ عَلَيْهَا وَهُمْ أَبْنَاءُ عَشْرِ سِنِينَ وَفَرِّقُوا بَيْنَهُمْ فِي الْمَضَاجِعِ)).
7)Fuskantar alqibla
(قَدۡ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجۡهِكَ فِی ٱلسَّمَاۤءِۖ فَلَنُوَلِّیَنَّكَ قِبۡلَةࣰ تَرۡضَىٰهَاۚ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَیۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّوا۟ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥۗ وَإِنَّ ٱلَّذِینَ أُوتُوا۟ ٱلۡكِتَـٰبَ لَیَعۡلَمُونَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَـٰفِلٍ عَمَّا یَعۡمَلُونَ)
[Surah Al-Baqarah 144]
8)Tsarki
عَنْ أَبِيهِ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((لاَ صَلاَةَ لِمَنْ لاَ وُضُوءَ لَهُ وَلاَ وُضُوءَ لِمَنْ لَمْ يَذْكُرِ اسْمَ اللَّهِ تَعَالَى عَلَيْهِ)).
9)Yarda da amintuwa da wajabcin sallah
عن عثمان رضي الله عنه أنه قال: سمعت رسول الله - صلى الله عليه وسلم - يقول:
"من توضأ فأسبغ الوضوء، ثم مشى إلى صلاة مكتوبة، فصلاها مع الإمام؛ غفر له ذنبه".
10)Suturce al'aura
(۞ یَـٰبَنِیۤ ءَادَمَ خُذُوا۟ زِینَتَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدࣲ وَكُلُوا۟ وَٱشۡرَبُوا۟ وَلَا تُسۡرِفُوۤا۟ۚ إِنَّهُۥ لَا یُحِبُّ ٱلۡمُسۡرِفِینَ)
[Surah Al-A'raf 31]
Allah ya taimake ka ya ƙara maka kwadayin ilmi mai amfani.
Daga ƙarshen ƴan uwa, kar mu manta cewa wannan sabubban karɓa ne kawai, sai sun cika kafin ayi maganar karɓa ko rashin ta, wacce kamar yadda ya gabata, ganin dama ne Allah, Allah yace
(۞........ قَالَ إِنَّمَا یَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِینَ)
[Surah Al-Ma'idah 27]
A nan kuma Allah yace
(... فَلَا تُزَكُّوۤا۟ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰۤ)
[Surah An-Najm 32]
Allahummaj alna minal muttaqin.
Wallahu ta'aala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*