*_HAILA TA ZO MATA SAURA MINTI 3 RANA TA FADI?_*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum, Malam tambayata ita ce mata ce ta yi azumi har saura minti 3 a kira sallah magariba sai jinin hailarta ya zo. To tambayata a nan ita ce, wannan azuminta na wannan ranan yana nan ko zata biya bayan sallah?. Allah Ya karawa Malamanmu basira.
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, in har jinin hailar ya fito a wancan lokacin da ka ambata, to azumin ta ya karye.
Saboda azumi yana kammala ne bayan faduwar rana, ita kuma na ta ya warware kafin lokacin, wannan yasa za ta rama bayan sallah.
Allah ne mafi sani.
01/06/2017.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.