HALLACCIN ADDU'A DA HAUSA A SUJJADA

*_HALLACIN ADDU'A DA HAUSA A SUJJADA!!_*

                               *Tambaya:*
Assalamu alaikum. akramakallahu mutum zai iya yin adduar neman wani abu a sujudar sallar farilla da wani yare koma bayan larabci?

                                    *Amsa*
To dan'uwa Annabi S.A.W yana cewa: "Amma sujjada to ku dage da addu'a saboda ya kusa a amsa muku" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 479.
Malamai sun yi sabani akan yin addu'a a sujjada da yaran da ba larabci ba, amma zance mafi inganci shi ne halaccin yin addu'ar da take ta neman wani abu a wajan Allah da yaran da ba larabci ba ga wanda bai iya larabci ba, saboda Allah ba ya kallafawa rai sai abin da za ta iya, sannan kuma Allah yana gane duk yaren da mutum ya yi addu'a da shi, amma wasu malaman sun karhanta yin zikirorin da suka zo a hadisi da yaran da ba larabci, saboda Annabi S.A.W ya fade su ne don su zama ibada, wannan yasa ba za'a canza su da wasu lafuzan ba.

Duba :Muhallah na Ibnu hazm 4\159 da Majmu'ul fataawa na Ibnu-taimiyya 22\488.

Allah ne mafi Sani

5/2/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)