HUKUNCIN FITAR MAZIYYI DA SHA'AWA BAYA KARYA AZUMI

*_HUKUNCIN FITAR MAZIYYI DA SHA'AWA BAYA KARYA AZUMI_*

                              *Tambaya:*
Idan mutum ya yi sumba alhalin yana azumi, ko kuma ya kalli wassu finafinai na tsiraici, sai maziyyi ya fito masa, Shin akwai ramuko akansa? Idan hakan ya kasance a cikin kwanaki mabanbanta, shin ramukon dole ne ya zama a jejjere, ko za a iya yinsu a rarrabe? Allah ya muku sakayya da mafi alherin sakamako, saboda hidima ga musulunci!

                                     *Amsa:*
👉 Fitan maziyyi baya lalata azumi a maganar da ta fi inganci daga cikin maganganun maluma guda biyu, lamarin haka ya ke sawa'un ya fita ne saboda sunbantar mata, ko kuma ta hanyar kallon finafinai, ko kuma makamantan haka, daga cikin abubuwan da su ke tada sha'awa, Sai dai kuma baya halatta ga musulmi ya kalli finanan tsiraici da batsa, ko kuma sauraron abin da Allah ya haramta na sauraron waqoqi, ko kayan kade-kade.

Amma fitar maniyyi da sha'awa kuma to shi yana lalata azumi; sawa'un hakan ya auku ne sakamako runguma ko sumbanta ko maimaita kallo, ko makamancin haka daga cikin sabbuban da su ke tada sha'awa; Kamar wasan fitar da maniyyi (istimna'i), da makamancinsa.

Mafarki da tunani, su kuma azumi ba ya baci da su, koda kuwa maniyyi ya fita da sababinsu.

👉 Kuma ba dole ne jerantawa wajen ramukon azumin ramadana ba, hasali ma ya halatta a rarrabe hakan, saboda gamewar fadin Allah Ta'alah: 👇

"Duk wanda ya kasance maras lafiya daga cikinku, ko akan tafiya to sai ya qididdigi wasu yinin na daban" _[Baqara: 184]._

ALLAH NE MAFI SANI.

*👉 FATAWA ISLAMIYYAH, MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 267).*

*_Abdallah A Abdallah Assalafeey_*

Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

1 Comments

Post a Comment