HUKUNCIN CEWA MALAMI (RADIYALLAHU ANHU)

*_HUKUNCIN CEWA MALAMI (RADIYALLAHU ANHU)_*

                                *Tambaya*
Assalamu alaikum malam Shin ya halasta ace ma wani babban sheikh ko malamin da ake ganin rikonsa da addini sosai (radiyallahu anhu?) bayan rasuwarsa?

                                    *Amsa*
Wa'alaikumus salam Mafiya yawan malamai sun tafi akan hallacin haka, kamar yadda Nawawy ya fada a Majmu'u, sharhin Muhazzab, saidai abin da ya fi shahara shi ne sahabbai kawai ake fadawa wannan jumlar, wanda kuma ba sahabi ba, ana ce masa (RAHIMAHULLAHU), in kuma yana raye (HAFIZAHULLAHU)

Allah ne mafi sani.

3/6/2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)