HUKUNCIN JININ ƁARI

*_HUKUNCIN JININ BARI._*


                           *Tambaya*
Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, Dan Allah idan mace ta yi barin ciki na wata biyu wannan jinin ya zaka na ciwo ko zata daina azumi sallah


                              *Amsa*
To dan'uwa wannan jini ba zai hana sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa ba ne, malamai suna cewa: duk cikin da ya zube kafin halittar mutum ta bayyana, to ba zai hana sallah da azumi ba, halittar mutum tana bayyana ne daga 80-90 daga samuwar ciki, saboda haka duk cikin ya da ya zube kafin haka, to jininsa, ba zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa ta fara bayyana, to za'a bar sallah da azumi.

Allah ne mafi sani.

30/11/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)