_*HUKUNCIN WANDA YA KALLI MATARSA YA FITAR DA MANIYYI ALHALI YANA AZUMI*_
*Tambaya*
Menene hukuncin wanda yakalli matarsa ba tare da ya taba ta ba, sai ya fitar da maniyyi alhali yana azumi?
*Amsa:*
Haqiqa wanda ya samu kansa a irin wannan halin zai cigaba da azuminsa, kuma ba ramuwa ba kaffara akansa. Dalili akan haka shine fadin Jābir Ibn Zaid cewa:"Wanda ya kalli matarsa ba tare da ya tabata ba, sai ya fitar da maniyyi, to,ya cigaba da azuminsa, babu komai akansa"
Haka kuma Abu Hanifah da Imamus Thaurī da Imamul Auza’i da Imamus Shafi’ī sun tafi akan haka Kuma sunce:Wanda ya sunbaci matarsa, sai yayi maziyyi alhali yana azumi, to, babu ramuwa kuma babu kaffara akansa.
Sai dai Imamu Malik yace: fitar maniyyi ta hanyar kalloko runguma yana karya azumi, kuma akwai kaffara akan haka. Amma idan maziyyi ne kawai, ramuwa za ayi ba tare da kaffara ba. Ya kafa hujja da cewa abin da ake buqata a jima’i shine fitar maniyyi. Saboda haka fitar maniyyi ta wannan hanya dai dai yake da jima’i.
Amma sauran malamai sun tafi akan cewa hukuncin danassi yazo dashi ya ambaci jima`i ne kawai, ba fitar da maniyyi ba. Sannan suka qara da cewa idan da mutum zai yi jima`i ba tare da ya fitar da maniyyi ba, ai zai rama azumi ne kuma yayi kaffara. Haka kuma, da ace fitar da maniyyi ne kawai ake lura dashi, sai ace mai barci ma idan yayi mafarki, ya fitar da maniyyi, sai yayikaffara.
ALLAH NE MAFI SANI.
✍ *Shashen Fatawowin Azumi a bisa Qur'ani da Sunnah*
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp._*HUKUNCIN WANDA YA KALLI MATARSA YA FITAR DA MANIYYI ALHALI YANA AZUMI*_
*Tambaya*
Menene hukuncin wanda yakalli matarsa ba tare da ya taba ta ba, sai ya fitar da maniyyi alhali yana azumi?
*Amsa:*
Haqiqa wanda ya samu kansa a irin wannan halin zai cigaba da azuminsa, kuma ba ramuwa ba kaffara akansa. Dalili akan haka shine fadin Jābir Ibn Zaid cewa:"Wanda ya kalli matarsa ba tare da ya tabata ba, sai ya fitar da maniyyi, to,ya cigaba da azuminsa, babu komai akansa"
Haka kuma Abu Hanifah da Imamus Thaurī da Imamul Auza’i da Imamus Shafi’ī sun tafi akan haka Kuma sunce:Wanda ya sunbaci matarsa, sai yayi maziyyi alhali yana azumi, to, babu ramuwa kuma babu kaffara akansa.
Sai dai Imamu Malik yace: fitar maniyyi ta hanyar kalloko runguma yana karya azumi, kuma akwai kaffara akan haka. Amma idan maziyyi ne kawai, ramuwa za ayi ba tare da kaffara ba. Ya kafa hujja da cewa abin da ake buqata a jima’i shine fitar maniyyi. Saboda haka fitar maniyyi ta wannan hanya dai dai yake da jima’i.
Amma sauran malamai sun tafi akan cewa hukuncin danassi yazo dashi ya ambaci jima`i ne kawai, ba fitar da maniyyi ba. Sannan suka qara da cewa idan da mutum zai yi jima`i ba tare da ya fitar da maniyyi ba, ai zai rama azumi ne kuma yayi kaffara. Haka kuma, da ace fitar da maniyyi ne kawai ake lura dashi, sai ace mai barci ma idan yayi mafarki, ya fitar da maniyyi, sai yayikaffara.
ALLAH NE MAFI SANI.
✍ *Shashen Fatawowin Azumi a bisa Qur'ani da Sunnah*
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.