IDAN MUTUM YANA CIKIN YIN SAHUR SAI YAJI AN KIRA SALLA YA ZAI YI?

_*IDAN MUTUM YANA CIKIN YIN SAHUR SAI YAJI KIRAN SALLAH YAYA ZAIYI??*_

                             *Tambaya*
Idan mutum yana cikin yin sahur, sai yaji kiran sallah yaya zaiyi?


                                    *Amsa:*
A irin wannan halin mutum zai qara sa abin da ke hannunsa ne. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira yace: Manzon Allah yace: *"Idan dayanku ya ji kiran sallah alhali qwarya tana hannunsa, kada ya ajiyeta, har sai ya biya buqatarsa."*

Amma anan sai ayi hattara, kada amayar da irin wannan dabi'a tazama al'adar kullum.

WALLAHU A'ALAM.

Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)