INA AIKI DA TAKARDUN बोगी, MEYE SHAWARA?

*_INA AIKI DA TAKARDUN BOGE, MEYE SHAWARA?_*

                               *Tambaya*
Assalamu alaikum, Mallam wata kanwar mu ce tayi karatu sai a final Din su suka  samu matsala board da yawansu.

Mallam ta fara aiki da takardan boge, Kafin taje ta gyara nata, yanzu haka takardar (original results) din na hannu tana so a Cire wancan a file din ta ayi replacing da da shi.
Shi ne take son ji ya matsayin kudin da take amsa tunda ba da takardan Gaskiya take aiki ba, kuma shin Zata iya ci gaba da aikin Idan ansa original din a file dinta?
Don Allah Mallam a taimaka mana

                                  *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Hukuncin wannan a fili yake @ zauran Fiqhu, ai Haram ta ci karara, tun ba da hakkinta aka bata ba.

Ana daukar aiki ne akan yanayin takardun mutum da gwargwadonsu, in har aka gina aiki akan karya, to duk abin da aka samu ta hanyar haka haram aka ci.

Allah ya kare mu daga cin hakkin daba namu ba.

Allah shine mafi sani.

3/04/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)