KO KA SAN AL-ƘUR'ANI ZAI YI CETON MA'ABOTAN SHI RANAR AL-ƘIYAMA?

*_KO KASAN ALQUR'ANI ZAIYI CETON MA'ABOTANSHI RANAR ALQIYAMA?_*
.
.
.
"An karbo daga Abu Umaamah Albaahiliy yace: Naji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa: " Ku karanta Alqur'ani don zai zo ranar alqiyama yana mai ceton ma'abotanshi."
(Muslim)

Wanda ya ajiye tilawa yayi maza ya dawo ya cigaba da tilawarshi ba dare ba rana.
Wanda bashi da tsari na tilawa arana toh ya dage yayi kuma ya kiyayeshi.

Ka tashi cikin dare mutane na barci kayi ibada to lallai hakan akwoi riban gaske.
Cikin shagulgulanka ka warema Alqur'ani lokacinsa.

Kina nan kin duqufa karatun littafan hausa, da kallace kallacen finafinai, anyi magana kince wai ba abin yi kana zaune shiru! ki kiyayi kanki da bata lokaci a aikin banza!

Abin mamaki wani sai ya zauna yaita cewa wai duk ya gaji bashi da abunyi? Yana nan jin wake wake da kallace kallace, zantuka marasa amfani! shin a ina ka aje Qur'aninka? ka manta zikirine? ko har ka gama tanadin guzurinka ne?

Kar ka kuskura ka bar Qur'ani duk rintsi don cikin yawan tilawar qur'ani tare da tadabburin ma'anoninsa, kiyayeshi ba dare ba rana, aiki dashi, yanada wani dadi da natsuwa dake mantar dakai dukkan wahalhalun rayuwa, damuwa، dagulewan al'amura, baqin ciki da sauransu.

♡Ga kuma tarin Laada ko wane harafi daya lada goma. zaka iya qirga yawan ladan? Kaga yanda Ubangiji keso ma bayinsa rahamarsa sai wanda yaqi.
Shaikhul Islam bnTaimiyyah Allah ya masa rahama yace: Banga wani abu da yake gyara hankali da ruhi, kuma yake kiyaye jiki, sannan yake qunshe da farinciki fiye da lizimtar kallon littafin Allah.

'Yan uwa mu yi kokarin ribatan lokutanmu ga ababen da zasu amfanemu.

Allah ya datar damu.

Rubutawa:- Umar Surajo Abu khadeejah
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)