*_KASHE-KASHEN HAKURI_*
*Tambaya:*
Malam ina son karin bayani game da Ire-iren hakuri?
*Amsa:*
To dan'uwa hakuri kashi uku ne
1. Hakuri akan biyayya ga Allah, sau da yawa mutum zai ji wahala da nauyi wajan aikata wasu daga cikin abubuwan da Allah ya umarce shi da su, kamar yin alwala da kuma sallar asuba a lokacin tsananin sanyi, da fitowa sallar azahar a lokacin da ake tsananin zafi, dole sai ya yi hakuri da juriya kafin ya iya aikatawa.
2. Hakuri wajan barin abin da Allah ya hana, sau da yawa zuciyar mutum za ta ji tana sha'awar abin da Allah ya haramta, duk wanda ya yi hakuri ya bar abin da Allah ya hana, to zai ba shi mafi alkairinsa a Lahira, wanda ya bar giyar duniya mai wari Allah zai shayar da shi giyar lahira mai kamshi, wanda ya bar matan banza masu kwailin a duniya Allah zai aura masa matan aljanna tsarkaka, kyawawa masu manyan ido, wadanda wani namiji kafin shi bai taba taba su ba, idan 'yan aljanna su ka shiga aljanna mala'iku za su shiga wajansu, su ce musu "Amincin Allah ya tabbata a gare ku, saboda hakurin da kuka yi (akan abin da Allah ya umarta da barin abin da Allah ya hana)" suratu Arra'ad aya ta 24.
3. Hakuri akan musifu da bala'o'in da Allah ya jarabceka da su, duniya gida ne na jarrabawa, duk lokacin da farin ciki ya sameka sai ka godewa Allah ka samu lada, idan bakin ciki ya sameka ka yi hakuri sai ka samu lada, dole ne mutum ya yi imani da kaddara komai dacinta, kuma imaninsa ba zai cika ba sai ya yarda da ita.
Allah yana jarrabar mutum gwargwadon imaninsa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa "wadanda aka fi jarraba sune Annabawa, sai kuma wadanda suke bin su wajan nagarta, haka dai zuwa wadanda suke bi"
Tirmizi da Ibnu Hibban.
Ka zama mai hakuri akan duka wadannan guda ukun, Allah yana cewa: "Ana cikawa masu hakuri ladansu ba tare da kidayawa ba"
Suratu Azzumar aya ta 10.
Allah ne mafi sani
25/9/2012
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_______________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.