LABARAI A TAƘAICE NA YAU

*LABARAI A TAKAICE*

*Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Abuja ta kama ‘yan Shi’a mabiya Ibrahim Elzakzaky 400 da su ka gudanar da muzaharar neman a saki shugaban na su da ke hannun jami’an tsaro tun disambar 2015.*

*Tun gabanin arangamar ‘yan Shi’an da ‘yan sandan, jami’an ‘yan sanda sun kama matasa biyu ‘yan Shi’a da su ka nufo Abuja da bom din kwalba 31 don niyyar wurgawa jami’an tsaron. ‘Yan sandan sun tara ‘yan Shi’a da su ka kama 400 a ofishin su da ke anguwar Garki don ci gaba da bincike da gurfanar da wadanda a ka samu da laifi gaban kotu.*

*‘Yan sandan sun zargi ‘yan Shi’an da kona motar ‘yan sanda. A kwanakin nan an samu arangama tsakanin ‘yan Shi’an da sojoji inda ‘yan Shi’a da dama su ka rasa ran su. An fara samun rasa rayukan ranar asabar a yankin Zuba da ke jihar Neja inda arangamar ta jawo harbe ‘yan Shi’a 6.*

*Babbar kotun taraiyar Najeriya ta dage ci gaba da sauraron karar da wani mutum mai suna Kanmi Ajibola ya shigar da ke nuna shugaba Buhari bai cancanci tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba don bai kammala karatun sakandare ba ko ba shi da takardar kammala karatun.*

*Mutumin dai lauya ne da kuma ya shigar da karar a babbar kotun taraiyar Najeriya da ke Osogbo jihar Osun don kalubalantar karar neman tazarcen shugaba Buhari. Dama wannan batu ya taba tasowa gabanin zaben 2015 inda rundunar sojan Najeriya ta baiyana cewa ba ta ga takardar ta kammala karatun shugaba Buhari ba.*

*Laftanar Janar Akinrinade mai ritaya ya zaiyana lamarin da cewa abun takaici a rika tada irin wannan magana ga mutum irin shugaba Buhari da ya taba mulki Najeriya. Manyan jami’an soja na zamanin baya na da irin wannan ra’ayi na daukar masu kawo irin wannan magana da rashin sanin ya kamata.*

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje ga al’ummar jihar Kaduna kan fitinar da ta yi sanadiyyar rasa rayukan jama’a ciki har da yadda masu satar mutane su ka sace Sarkin Adara Mr. Galadima da kuma yi ma sa kisan gilla.*

*Wannan na faruwa yayin da jami’an tsaro su ka damke mutum 93 da a ke tuhuma da hannu a tada fitinar. Shugaban ya yi fatar za a hukunta masu laifi don aminta al’umma daga miyagun iri.*

*Kasar Denmark ta dawo da jakadan ta na Iran gida don samun iran din da laifin yunkurin kashe wani dan gwagwarmayar Larabawa da ke adawa da Iran din a kasar ta Denmark. Denmark ta ce sam ba za ta yarda hukumar bayanan sirri ta Iran ta kai wa ‘yan adawa hari a kasar ta ba.*

      
          
            *21st-Safar-1440Ah*
            *31st-October-2018*
Post a Comment (0)