*LABARAI A TAKAICE*
*Rahotanni na baiyana janye hana yawon rana a Kaduna, Najeriya bayan dawo da dokar don hana sabuwar fitina sakamakon samun gawar Sarkin Adara da tun farko masu satar mutane su ka sace shi daga bisani miyagu su ka yi ma sa kisan gilla.*
*Daga litinin din nan mutane a garin Kaduna ka iya zirga-zirgar su daga karfe 6 na safe zuwa 5 na yamma. Wannan ya nuna kasuwanni da bankuna za su kasance a bude don hada-hadar kasuwanci da kuma sufuri a tashoshin mota.*
*Da alamu jami’an tsaro sun dau matakan tabbatar da tsaron rayukan matafiya da kan taso daga Abuja zuwa Kaduna musamman yankin Gonin Gora da a kan samu miyagun iri.*
*Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin Buhari tun da ta hau mulki a Mayun 2015, dala biliyan 10 ta ciwo bashi, ya na mai nanata cewa cin hanci da rashawa kan zabge kudin Najeriya.*
*Osinbajo da ke magana a wani taro a jami’ar Ibadan ya ce hakan ya sanya jumillar bashi da a ke bin Najeriya yanzu dala biliyan 73 ne don gwamnatin ta Buhari ta gaji bashin dala biliyan 63 ne. Mataimakin shugaban ya kara da cewa Najeriya ba ta taba samun kudi mafi yawa da ya wuce na tsakanin shekara ta 2010-2014.*
*Farfesa Osinbanjo ya caccaki masu neman a yi wa Najeriya garambawul na tsarin zaman kasa, ya na mai cewa masu yada maganar na boye gazawar su ta rashin yin hakan ne lokacin da su ke kan mulki. Ba mamaki Osinbajo na gugar zana ne ga mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar da ke yada wannan magana ta garambawul.*
*Daidai lokacin da a ke muhawara kan karbar sunayen ‘yan takarar zaben 2019 na APC daga Zamfara, shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ya ce hukumar ba za ta ce komai ba tun da wadanda lamarin ya shafa sun kai kara kotu, amma sam hukumar ba ta karbi sunayen ba.*
*Farfesa Yakubu na magana ne kan rade-radin jam’iyyar APC ta mika sunayen ‘yan takarar ta daga kan na gwamna zuwa ‘yan majalisar dattawa da wakilai da tun farko hukumar ta ce ba za ta amshi sunayen ba don saba ka’idar lokacin gudanar da zaben.*
*Jigo a siyasar APC ta Zamfara Ikra Aliyu Bilbis ya ce sun kalubalanci matsayin hukumar zaben a kotu don su na da yakinin an gudanar da zaben, da sa ran samun hukunci a talatar nan. Tun a tarihi in hukumar zaben ta dau mataki kan lamari irin wannan, kotu ce kan zama raba gardama kuma ko ma ta yaya shari’ar ta kaya, ba mamaki wanda bai gamsu ba ya tafi kotun daukaka kara.*
*Manyan kasashen duniya 4 sun yi taro a Istanbul na Turkiyya inda su ka sha alwashin samo bakin zaren salama a kasar Sham. Kasashen sun hada da Faransa, Jamus, Rasha da Turkiyya. Kasashen sun ce za su dau matakan sulhun ta makomar Idlib da yanzu itace tungar karshe ta ‘yan tawayen Sham.*
*19th-Safar-1440Ah*
*29th-October-2018*