LIMAMIN DA YA SHA MARI A BANZA

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA �*
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_

*DRS NA 014*
*LIMAMIN DA YA SHA MARI A BANZA*
Wani limami ne ya kawo kara a wurin Sarki, wani talaka ya mare shi. A fusace Sarki ya sa aka nemo shi. Da talakan ya zo Sarki ya daka masa tsawa yana tambayar sa, me ya sa ka mari Liman? Sai ya
sunkuyar da kansa ya ce, Allah ya taimaki Sarki, a sallar asuba ne ya ja mana karatu mai tsawo har duk muka takura kamar yana sallar alkayeji (tarawihi), bai sallama ba sai da rana ta kusa fitowa. Bayan ya
sallama kuma sai ya ce da mu duk ku sake sallah domin na manta ban yi alwala ba! Ai kuwa nan take sai Sarki ya harari Liman, ya ce, ai kuwa
lallai Liman ka sha mari a banza. Gobe ma sai ka kara!

Darasi: Idan ba ka da gaskiya kowa ma sai ya fita batun ka. �
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.

Post a Comment (0)