RIƘON AMANA

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA �*
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_

*DRS NA 015*

*RIKON AMANA*
A cikin kundin tarihin magabata mun samu labarin wani amintaccen marubuci da aka yi a kasar Andalusiya tun farkon karni na bakwai na Hijira. A wancan lokaci rubuta littafai babbar sana’a ce wadda ake tutiya da ita. Wannan bawan Allah sunansa Muhammad
Ibnu Gaddus. Babban aikinsa shi ne rubuta Alqur’anai. Kasancewar babu madaba’a a wancan lokaci, ga shi kuma da kyakkyawan rubutu,
da iya sanya kalolin tawada wadanda suka dace a kan surori da ayoyi, wannan ya sa mutane sukan zo wurin sa daga gari-wa-gari, sarakuna
kuma sukan yi layi wajen jiran sa ya qare don a saya. An ce ya rubuta Alqur’anai da hannunsa wadanda ba za su kasa dubu daya ba. Kuma
saboda ficen da ya yi a wannan fanni, Alqur’anin da ya rubuta ana sayar da shi sama da Dinari dari biyu, kudin da ba kowa ne ya mallake su ba a wancan lokaci. �
An hikaito cewa, saboda tsare amanarsa, idan ya kammala rubuta Alqur’ani sai ya karance shi tukuna don ya tabbatar da babu wani kuskure a cikin sa sannan ya sayar da shi. Watarana ya kammala rubutawa kuma ya yi bitar sa kamar yadda ya saba sai ya tarar da wani
digo guda daya da ya tsallake bai rubuta shi ba, amma sai ya yi jinkiri har ya manta, kuma aka yi sa’a wani mutum ya zo neman Alqur’ani daga yankin yamma sai ya saida masa da shi, daga bisani ya tuna cewa, ya manta wannan digo bayan mutumin ya tafiyar sa. A nan ne fa ya shirya tafiya zuwa garin da wannan mutumin yake. Sai da ya kwana
arba’in a kan hanya sannan ya isa. Da ya je ya neme shi ya gyara masa rubutun Alqur’aninsa ta hanyar sanya wannan digo da ya manta
sannan ya dawowar sa.

*Darussa:*
▶ Na Allah ba su karewa har duniya ta kare

▶ A da, mutane suna shan wuya kafin su yi ilimi fiye da yau. Ga kuma hanyoyin sadarwa masu yawa da muke da su. Domin idan a yau ne, ko dai ya hau mota a cikin kwanaki uku ya je ya dawo, ko ma ya buga masa waya kawai ya ce, ka rubuta digo a wuri kaza.
Kai, a yau ma ko kuskuren ba a samu saboda kofi guda ne ake gyarawa sai madaba’a ta buga miliyoyi irin sa.

▶ Addinin nan da wahala aka iso mana da shi. Bai dace mu kasa yin kokarin isar da shi ga na bayanmu ba. �
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.

Post a Comment (0)