MAIRO 06

♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*6*

tun daga lokacin Gwaggo bata sake bari Mairo ta fita ba.
tallar da take ɗora mata ma bata sake ba kullum tana gida ko fita zatayi saida tare da Gwaggo,

tun abun baya damun Mairo har ya fara damunta
tunani take ko ta saci hanya ta fita in kuma ta tuna da dukan da Halilu yayi mata saita tsorata duk da yake tasan Gwaggo tace mata ba zata sake bari ya dake taba.
tana zaune ta raffka uban tagumi tana tunanin karyar da zatayiwa Gwaggo da zata sa ta kyaleta ta barta fita,
can wata dabara tazo mata
tashi tayi ta koma kofar ɗakin gwaggo ta fasa kuka tana murgemurge
da sauri Gwaggo ta fito tana tamabayarta “lafiya Mairo mi nene?”
“ni gidansu Jummala nake son zuwa ba tada lafiya”
shiru Gwaggo tayi tana kallonta dan tasan rigimar ce ta tashi
“nidai babu ruwana kinsan halin Halilu in yanxu yazo bai ganki ba faɗa zaiyi”
“tho ai ba daɗewa zanyi ba kuma ai ba zaki faɗa masa ba”
Gwaggo bata sake cewa komai ba ta nufi tabarma ta zauna.
Mairo na ganin haka takara ɗaga murya tana ihu
cikin faɗa Gwaggo tace “tashi kije kuma duk kika daɗe babu ruwa daga can kuma karki biya ko ina”
tashi tayi tana dariya daman kukan kawai take ba hawaye.
“amman dai zan biya giɗan tsoho ko tunda kusa ne”
“nidai ba ruwana keda Halilu”
“eh na yarda”
da gudu ta fita gidan

bata tsaya ko'ina ba sai gidansu jummala wuni sukayi suna shiririta basu can basu nan.
sai da bayan magariba sannan ko wannensu ya nufi gida
da fargaba ta shiga gidan tana lek'e2
bakin k'ofar ɗakin Gwaggo ta hango Halilu zaune farin wata na haskashi.
faɗuwa gabanta yayi ɗan tasan ita yake jira zagi ta shiga zabga masa cikin ransa.
_hege mai katon kai mai kamada zabarmawa ni dai wlh ka takuramin Allah kasa ma ya mutu mai idon mage (mussa) mai kan ɓera_
ta daɗe gurin tsaye tana kallonsa wai ko zai tashi amman sai kara gyara zama yake.
kamar ta fasa kuka ta shiga kwalawa Gwaggo kira _Gwaggo Gwaggo Gwaggo a dawo_
ɗagowa Halilu yayi yana kallon k'ofa yace “to shigo mana aike ake jira”
k'in shigowa tayi ta cigaba da kwalawa Gwaggo kira “Gwaggo ke ki taho mana gani”
ta daɗe tana kiranta sannan ta fito sanye da hijab da alama sallah ta k'are,
har kofar gida tazo ta kama hannunta suka shigo.
tashi Halilu yayi yana k'ok'arin rikota Gwaggo ta tare “kyaleta Halilu ni na aiketa”
“Gwaggo ki daina goya mata baya tana k'ara lalacewa”
“tho mi nayi da zakace na goya mata baya bana son raini fa Halilu”
“wane irin aikene zaki mata tun da maraice sai dare zata dawo”
Mairo ta turo baki tana watsa mata harara “ai bada maraice bane da rana ne”
buge mata baki Gwaggo tayi “ke yiwa mutane shiru dake ake ne”
kai Halilu ya girgiza “yayi miki kyau ai kamaki zanyi saiki faɗi wadda ya aikeke”
kuka Mairo tasa “Gwaggo kinji ko dukana zaiyi”
“ba zai dakeki ba bani na aikeki ba”
“hmmm Gwaggo ina miki tsoron wata rana ki daina goyawa Mairo”
“wai miyasa ka rai nanine Halilu karya zan maka kenan na faɗa maka aikenta nayi”
taɓe baki yayi ya girgiza kai ya fice.

kwafa tayi da taga ya fice “kai mugu bakin azzalumi to zo ka dakeni ɗin”
sakin hannunta Gwaggo tayi ta shiga mata masifa “ban rabaki da rashin kunya ba kuma kinsan saida mukayi dake bazaki daɗe ba kikaje kika zauna har dare”
turo baki tayi “to ba shine daren yayi saurin yi ba kuma kinsan na daɗe ban fita ba kuma...”
bata karasa maganar ba Gwaggo ta katsa mata tsawa “ke dan Allah rufe min baki 'yar rashin ji kuma ki wuce kije kiyi sallah kici abinci”
da ture2 ta nufi ɗaki tana gunguni.

_Washe gari..._
tun safe Mairo tasa Gwaggo gaba tana rokonta tayi mata giɗar siyarwa,
sai faman rantsuwa take mata wai bazata sake yin abunda tayi ba.
sam Gwaggo kin yarda tayi duk da magiyar da tayi ta mata
Mairo na ganin haka ta sawa Gwaggo kuka ba k'akkautawa harda su shak'ewa tana murje murje cikin kasa duk ta bata kayan jikinta.
banza Gwaggo tayi da ita duk da bata son kukanta amman ta daure.
haka ta wuni tana kuka ta kuma yi sa ah Halilu bai dawo gidan ba tun fitar da yayi da safe. 
          saida ta gaji dan kanta ta shi ta dawo kusa da Gwaggo dake tukin tuwo ta zauna tana ajiyar numfashi,

    Gwaggo saida ta gama kwashe tuwon ta kai ɗaki sannan ta riko hannunta suka shiga banɗaki tayi mata wanka.
har suka fito bata daina ajiyar zuciya ba idanuwanta duk sun kunbura sunyi ja
saman gado Gwaggo ta zaunar da ita ta ɗauko doguwar rigar atamfa tasa mata,
ta kwantar da ita saman jikinta tana shafa bayanta
lafewa Mairo tayi in banda ajiyar zuciya babu abunda take sauke
sun daɗe a haka Gwaggo sai buga mata baya take tana son tayi bachi ita kuma taki tayi bachin sai faman sauke wahalallen numfashi take.
kai Gwaggo ta girgiza tace “ni kan Mairo kina bani mamaki ace bakida aiki sai kuka sai ja magana sai masifa haka kawai ki wahallarda kanki dubi yadda kika wuni kina kuka”
nan sabon kuka ya zo mata “to bake bace kika ki yarda kimin giɗa ba kuma na faɗa mki bazan sake ba”
da in'in niyar kuka take maganar tana numfashi da karfi kamar zuciyar zata fito

bubbuga bayanta Gwaggo ta shigayi tana faɗin “halinki nake tsoro Mairo karkije ki sake yin wani abun kuma kina ganin yadda Halilu ya sa miki ido jira kawai yake kiyi wani abun bama hHlilu kaɗai ba harda makota jiraye suke dake Mairo ke kuma gaki baki jin magana”
ɗagowa tayi idonta cike da hawaye tace “wlh Gwaggo na daina na faɗa miki bazan sake ba in kuma na sake Allah yasa na mutu”
rufe mata baki Gwaggo tayi “Subhanallahi Mairo miye haka karki sake faɗan irin wannan maganar kinji”
kai ta ɗaga mata “na daina Gwagho zaki doramin ko gobe zakimin giɗar?”
shiru Gwaggo tayi tana tunani dan tasan Halin Mairo in kuma bata dora mata ba wata sabuwar masifa ce.
kallonta tayi tace “kinmun Alkawari bazaki sake ba bazaki yi abunda zaisa a dake kiba?”
da sauri tace “eh nayi”
“shikenan zn dora miki”
“gobe ko Gwaggo?”
“eh Allah ya kaimu”
“amin”
rumgumeta tayi “na gode Gwaggo”
“Allah yayi miki Albarka”
“amin gwaggo zaki sayamin hancin ligidi?”
“eh  shi kike so?”
“eh”
“to bari na bada a siyo miki”
kwantar da ita Gwaggo tayi ta nufi kafit (wadurup ta da tsohuwar yayi) ta bude fanteka (kwala) ta ɗauko kuɗi ta sa hijabinta ta fice.

© *Khadeeja Candy*

Post a Comment (0)