MAIRO 07

♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*7*

_Washe gari..._
tun da asuba Mairo ta tashi tana yin sallah ta shiga karatun gajerun  surorin data iya inta kare ta sake maimaitawa har rana ta fito.

_8:14pm..._
Gwaggo na motsa kunu (koko) Halillu ya shigo gaishe ta har lokacin Mairo karatu take.
mamaki yayi sosai bayan sun gaisa da Gwaggo yace “yau yarki abun k'warai akeji?”
murmushi Gwaggo tayi “ai daman tana abun k'warai indai karatu ne ai kasan Mairo ba baya ba”
“a makarantan ba agida yaushe rabon da tayi irin wannan karatum tunfa da asuba nake jinyo ta ɗakina”
“to ai daman Mairo abunda take ai kuruciya ce data girma dainawa zatayi”
“ai da girmanta Gwaggo yanxu inta kara kaɗan ai aurarda ita za'ayi”

kuka Mairo ta fara wadda ba hawaye ta daina karantun “wlh Gwaggo bana son aure ba zanyi ba”
dariya Halilu yayi “au daman ba karatu kike ba kunnenki na kanmu ai daman nasan karatun munafirci ne”
kamar ta fasa kuka ta kalli Gwaggo “kice ya kyaleni ya tashi ya bar miki ɗakinki”
kofi Gwaggo ta janyo ta zubawa Halilu ta mika masa “karɓi ga kununka kosai na can gindin murhu a kwano”
dariya yayi bayan ya karɓa yace “dan tace ki koreni shine zaki koreni Gwaggo?”
“to naga fitina kake son jami muna zaman mu lafiya”
“ai ni gaskiya ce na faɗa kuma Mairo da kike gani aurene kawai zaiyi mata hankali ta daina abubuwan nan da take”
haɗashi da Allah Gwaggo ta shiga ganin Mairo nason yin kukan da gaske daker ta samu ya fita.
juyawa Mairo tayi zata cigaba da karatu Gwaggo ta shafa bayanta “taso haka yar Gwaggo ki karya (breakfast) ai kinyi karatun da yawa”
murmushi tayi “to gwaggo aI zaki mun giɗar ko?”
“sosai ma ai dole nayi miki bana miki alk'awari ba anjima kaɗan zanyi miki”
daɗi ne ya lumluɓe Mairo da sauri ta ɗauki kayan karatun ta aje gefe ta kwanto jikin Gwaggo ta soma bata kunun tana sha cike da jindaɗi.

_2:00pm....._
Mairo ta fita tallar giɗar k'inbi tayi hanyar da tabi ranar duk da zuciyarta na raya mata ta ɗan lek'a taga ko yana nan gashi har k'anshin goribar birni takeji tana tuna yadda take cinta.

haka dai ta daure ta nufi bakin kasuwa gurin data saba zama tana siyarda giɗar. wata yarinya na zaune a gurin tana ganin Mairo ta tashi da sauri ta koma gefe dan tasan halin Mairo indai matsifa ce saida ka barmata balle yau da fuskarta take a haɗe kamar anyi mata mutuwa.

koda la'asar tayi Mairo siyar da bakin rai ta nufo gida tana tureture baki kamar ta fasa kuka sai wata tafiya take kaɗan kaɗan.
haka ta ido gida ko sallama babu tun a bakin kofa tayi jifa da turen ta ta karaso idonta ciki da kwallah ta zauna kusa da Gwaggo dake Sallah,

tana sallamewa ta kalleta “lafiya Mairo waya taɓa ki?”
soshe soshe ta shiga yi tana tunano karyar da zatayi “ni..ni...ni....ɗan ta malele zan siya?”
shafa kanta Gwaggo tayi tana murmushi “haba Mairo sai kace wani abu harda su kwallah? ɗauki kuɗi kije ki siyo ki haɗa da kifi yadda zaki jidaɗin cinsa”
kai ta ɗaga “tho amman sai in zanje makaranta”
“tho inkin huta ki watsa ruwa sannan kije makaranta kinji”
kai ta ɗaga mata ta mika mata kuɗin giɗar.
“eyeee Mairo yau duka aka siyar gaske naji kin jefar da ture tun kofa”
murmushi Mairo tayi “yau nawa zaki ban?”
“hamsi zan baki ashiri kisa a susu talatin ki siye ɗan ta malele”
ta karasa maganar tare da mika mata 50 ɗin.,

da zumuɗi ta karɓa ta tashi ta nufi ɗaki da guɗu yau an sami abun sawa a susu mai tsoka.

    '''*** *** *** *** *** ***'''
     tun daga lokacin kullum sai Gwaggo tayiwa Mairo giɗa ita kuma bata fashin zuwa gurin siyarwa so ɗaya ta je gurinda aka bata goribar birni koda taje bata tararda kowa ba tsoro taji sosai babu abunda take rayawa a ranta sai aljani ne

“kai aljanine wannan mutunen da gaskiyar Gwaggo tunda gashi ban sake ganinshi ba kuma duk goriba karfine da ita amman tashi taushi ne da ita kuma na riga naci”
a fili take wannan maganar can ta tsaya tana tunani “inda ba aljani bane ai bazai zo cikin dajin nan ba har ya zauna kuma fa....”

bata karasa maganar ba ta watsa da gudu saboda motsin da taji cikin itacen dake gurin tana faɗin “karku biyoni na daina bazan sake zuwa ba wayyoh Gwaggo”
ihu take tayi da kuka tana gudu rabin giɗarta na zubewa,
har tabar gurin bata daina kuka ba dan gani take kamar sun biyota saida ta isa baki kasuwa sannan ta ɗan natsu ta soma numfasawa daidai,

tun daga lokacin bata kara tunanin zuwa gurin ba
duk ta ɗauko tallar giɗarta sai dai ta nufi bakin kasuwa inta siyar ta tayi ta shiririta ita da abokanin talla ko inta dawo ta biya gidansu jummala suyi gantalin da suka saba daman haka take so,

fagen neman magana da matsifa ba babba ba yaro kowa ta raina musamman inta ga ta girmeka ko kana tsoronta,
        Gwaggo in banda goya mata baya babu abunda take.
Halilu yayi faɗa harya gaji amman a banza kamar ma kara turata yake,

gashi Gwaggo ta hana ya daketa sai in ya faki idonta ko ya haɗu da ita can waje.
harta saba inta ganshi saita chanja hanya haka suka rika wasan ɓoya ita dashi.

*_3 months later....._*
yau da wuri Mairo ta siyarda giɗarta kuma yau bata jin wasa saboda dukan da Halilu yayi mata jiya dan yanzu har bakin kasuwa yake zuwa da ya tarar tana wasa ya fatattaketa da duka har gida,

duk yadda abokanin shashacinta sukaso ta tsaya kiyawa tayi dan tsan sai yazo gurin kuma Gwaggo tace mata da ta siyar ta dawo gida dan kar halilu ya daketa,
sallama tayi musu badan sunso ba dole suka kyaleta wasu kuma suka wuce gida dansu inba da Mairo ba basa jindaɗin wasa,

_Aysha adon gari ga Hajara adon gari ni Maryam adon gari inba ni ai ba gari Khadija Abubakar nake Candy kunji laqani gani tafe da'ayari yan mata a dandali_(MY UP COMING SONG INSHA ALLAH)
Mairo na tafe tana rera wak'a mak'ale da turenta na giɗa.

tunda kamin ta k'araso ta hango wata kafirar mota baqa mai shek'i fake kofar gidansu yara sun zagayeta sai shafa suke.

© *Khadeeja Candy*

Post a Comment (0)