♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*15*
tunda suka shiga motar Mairo kasa magana tayi saboda tsoro saima rike bel ɗin motar da tayi,
shima bai tanka mata ba saida suka kusa isa gida sannan ya soma magana ba tareda ya kalleta ba “ina kika sanshi Maryam?”
shiru tayi kamar ba zata amsa ba saida ya sake maimai tawa sannan tace “can gida na sanshi harda kuɗi yake bani da goribar bunni ba na taba faɗa maka wani yaban goriban bunni ba?”
kai ya ɗaga mata “eh ina ya haɗu dake?”
“can gida”
“gida ina?”
daidai nan suka iso gida yana yin parking ta yinkura zata taji bazata iya buɗewa ta juyo ta kalleshe “buɗe min zan fita”
yana kallon kallon fulawoyin gidan yace “sai kin faɗa min gurin da kika sanshi?”
kamar ta fasa kuka tace “bana ce maka can gida ba”
sai a lokacin ya kalleta “to ai baki min bayani yadda zan gane ba”
ganin babu sarki sai Allah dole tasa ta faɗa masa tun farkon haɗuwarsu,
“to tun daga lokacin baki sake ganin shi ba sai yanzu?”
“eh nidai buɗe min na fita”
“to ya akayi ya ganeki?”
“nidai ba shine ya ganeni ba ni ban saniba”
bai sake ce mata komai ba ya buɗe motar ya fita,
ya zagayo gefenta ya buɗe mata ta fito da guɗu ta nufi parlour. bayan ya rufe motar ya rufa mata baya,
parlour suka tararda momi da gudu Mairo ta faɗa jikinta “kinga yaya ya simin mai kyau”
dubawa Momi ta shigayi tana yabawa “eyyye yar yayanta duk ke kadai?”
“eh ni kuma na zaɓo kuma mukaje yawo”
“amman gaskiya yana ji dake to injin kin masa godiya?”
“eh na masa ko yaya?”
kai ya ɗaga mata yana murmushi
“eh kinyi bama iyaka”
“naji je ɗaki ki aje”
“to”
tashi tayi tana dariya ta nufi ɗakin.
momi ta kalli Qasin tace “magana nake son muyi dakai Qasin mai muhimmanci”
agogonsa ya kalla “owk momi amman fa kamar lokacin Sallah yayi”
agogon ɗakin momi ta kalla “inaga ma an soma sallar wani gurin jeka masallaci kawai nima bari na tashi nayi sallah gobe mayi maganar”
‘to’
kawai yace ya tashi ya fice jiki yake baya son maganar duk da bashi da masaniya akan abunda zasu tautauna,
*_washe gari....._*
da safe Qasin bai lek'a part ɗin momi ba ya wuce gurin aiki,
bai shigo gidan ba sai dare part ɗinsa ya fara wucewa saida yayi wanka ya sauke gajiya sannan ya nufo part ɗinta,
zaune ya tararda momi tana hamma Mairo na kasan carpet tana bachi Usman da Nura ma duk bachi suke saman kujera,
ta dasu Qasin yayi yana faɗa “momi sai ki rika barinsu suna miki bachi saman kujera manya dasu kuma maza”
“ai nasha musu magana har na gaji”
masifa Qasin yayits musu da suka farka basu dai ce masa uffan ba daya kare suka tashi kowane ya nufi ɗakinsa,
tsaki yaja ya zauna yana faɗin “shi yasa Siraj yake burgeni wlh shi halinsa da ban yake”
momi tace “ai Siraj yasan kansa gadai wata nan da take son biye musu”
kallon Mairo yayi “gaskiya momi ya kamata asa maryam makaranta dan inaga Gwaggo ba k'arɓarta zatayi ba”
“eh ai inaso ma maka maganar daman jira nake naga yadda zaman zai kasance dan kar asata daga baya tace abata yarta amman kaga yanxu tunda bata tambaya ba ai sai a sakata”
“ina gafa Gwaggo fushi ne tayi kinga ai ko waya bata kira duk da son da take yiwa Maryam”
“fushi kan ai da gani”
momi na yunkurin tashi Qasin yace “momi wace magana ce kikace zamuyi jiya?”
da idon bachi momi ta kalleshi “bachi zanyi ba wani magana yanzu yau ma ko leko nan bakayi ba bakayi breakfast ba ka fita”
“eh kirana akayi shiyasa kuma tunda naje nake aiki sai da magriba na samu kaina”
“to nidai bachi zanyi kuma ko gobe bani da time dan gobe abbanku zai dawo”
tashi yayi yasa hannayensa aljihu yana faɗin “Allah kawoshi lafiya ni bari naje na kwanta”
“to saida safe ta damun maryam kamin ka wuce”
ɗaki momi ta nufa tana hamma,
a hankali Qasin ya shiga data ita ganin bata motsaba yasa shi girgiza ta. ciki magagin bachi ta rika faɗin “mumi kinga Siraj ko”
“ba Siraj bane nine tashi kije ɗaki ki kwanta”
sake komawa tayi bachi haka yasashi data ita tsaye yana girgizawa “ke momi tace kije ɗaki ki kwanta”
“aa barni ni nan zan kwanta”
girgizata ya rikayi da karfi daker ya samu ta buɗe ido aiko tana ganin shine ta kara zube masa, dole ya ɗauketa ya kaita ɗakin yayiwa momi saida safe ya fuce.
*_4:21pm....._*
momi na zaune ita da Siraj suna fira sukaji an buga k'ofa. kofar momi ta kalla tace “waye?”
shiru akayi ba amsa nan ta kalli Siraj “jeka duba”
tashi yayi ya nufi kofar yana buɗewa yaga Yarima tsaye cikin kananan kaya yasa hannayensa ciki aljihu sai kanshin turare yake fuskarsa na kallon wani gurin.
kasa masa magana Siraj yayi shima kin juyo fuskar yayi ya kalleshi,
juyowa Siraj yayi ya nufi ɗakinsa tambayarsa momi ta shiga “lafiya wanene?”
yana gaf da shiga ɗakin yace “gashi nan waje nima ban sanshi ba”
tashi momi tayi ta nufi kofar, yadda Siraj haka ita ta tararda shi tsaye murmushi momi tayi tace “Yarima ne yau a gidan?”
sai a lokacin ya juyo ya kalleta shima fuskarsa ɗauke da murmushin “nine Momi”
“kuma ka tsaya a waje”
“to ai ba amin iso bane”
kai momi ta girgiza “Yarima ai naga gidan ba bakonka bane gidan nan ai gidanku ne tunda kai ɗana ne”
momi na cewa haka ta juyo ta dawo cikin parlour.
kai ya ɗaga yana karewa bakin kofar kallo kamar sannan ya taka kafarsa ya shiga cike da takama,
yana zaunawa momi ta dire mishi drinks.
“yau Yarima an tuna damu? kodai wani abun ne ya kawoka?”
da kanshi ya shiga zuba drinks ɗin yana faɗin “ziyara ce na kawo muku momi”
momi tayi dariya “aiko ka kyauta ya aiki to ya kuma gida?”
saida ya kurɓa drinks ɗin kusan so uku sannan yace “Alhamdulillah”
kallon parlour yake ta ko ina kamar mai neman wani abu.
can ya kalli momi yace “gaskiya momi Siraj bashi da tarbiya”
ko kaɗan momi bata jidaɗin maganar ba amman haka ta haɗiye tayi murmushi “yayan zamanine sai hakuri kannen naka”
taɓe baki yayi ya juyarda fuskar wani gefe.
momi zatayi magana Mairo ta fito kicin rike da abu a hannu tana faɗin “mumi kinga ni duk na wanke shuwakar kuma ta fita” maganar take tana kallon kujerar da Yarima yake zaune dan bata gane ko wanene ba,
momi tace “thom naji jiki gani nan zuwa”
yana juyowa suka hada ido murmushi ya sakar mata.
waje Mairo tayo da ido ta buɗe baki ta nufoshi da gudu rike da shiwakar da sauri momi ta tashi tsaye kamin ta rikota ta rumgumeshi har cup ɗin dake hannunshi ya faɗi.
Tags:
Littatafai (Novels)