MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*16*
fisgota momi tayi ta jefar k'asan carpet “lallai Maryam baki da hankali daga ganin mutun baki san inda ya fito ba ki wani rumgumeshi dubi yadda kika bata masa riga”
momi ta kalli yarima “dan Allah Yarima kayi hakuri hankaline bata da”
cikin kuka Mairo tace “nida hankalina niba mahaukaciya bace”
hannu momi ta ɗaga zata ɗaketa Yarima ya rik'e “no momi plz”
hannu yasa ya ɗago Mairo yana bata hakuri,
kuka Mairo tace yanzu ta fara daman mai nema a duhu balle an yada duk yadda yaso tayi shiru k'iyawa tayi.
fuskarta ya kama da hannayensa biu ya rik'e iya karfinsa ta kasa juya fuskarta shi kawai take kallo.
“yi shiru kinji in kina son na baki apple da abu mai daɗi”
kai ta ɗaga “to na daina”
“good girl”
handkerchief ya ciro ya share mata hawaye ya cire mata majina,
juyawa tayi tana hararar momi k'asak'asa ta gefe Yarima yayi murmushi ya rika hannunta ya “muje ki raka ni”
lakkame masa hannun tayi “ba kace zaka bani abun daɗi ba”
baice mata komai ba ya kalli momi yana murmushi yace “ni ban wuce momi in Qasin yazo ki gaishe shi”
fuska a sake momi ta amsa mishi “to zan faɗa miki mun gode a gaida gida”
kuɗi ya ciro masu ɗan dama ya aje mata sannan ya fice rike da hannun Mairo.
motarsa ya nufa harya buɗe rike yake da hannunta yana zaunawa ya kama ɗayan hannum ya rike “faɗa min miye dan gantakarki da gidan nan?”
turo masa baki tayi “to ni nasan mi kake nufi ne”
shiru yayi yana tunanin yadda zai mata ta gane “faɗa min momi mamar suwa ce?”
kai ta ɗaga sama “maman yaya da Siraj da Usman da Nura su kenan”
“good ke kuma ina mamanki?”
“mu bamuda mama sai dai Gwaggo tana can gida”
“yauwa to faɗa min ya akayi kika zo nan gidan?”
“da sukaje can suka zo dani nan gidan”
“to faɗa min Qasin yace miki wani abu da ya gamu tare?”
“a a baice komai ba”
banɗir ɗin 500 ya ciro ya dora mata saman hannu yana faɗin “karki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake kinji”
da karfi tace “to bazan faɗa ba” tana wani kallon kuɗi tana dariya.
har kasa ta duka tana masa godiya,
kunnenta ya kamo yana faɗin “duk kika faɗawa wani saina ɓata dake kuma bazan sake miki komai ba”
ɗagowa tayi tana kallonsa “wlh ba zan faɗa ba ko za a kasheni”
murmushi yayi “yauwa jeki kar moni taga kin daɗe”
tashi tayi da gudu ta nufi cikin gida.
saida yaga shigewarta sannan yayi ma motarsa key.
kaura suka tashi yi da Qasin daya kunno kai cikin gidan shi kuma yana k'ok'arin fita da sauri Qasin ya bashi hanya dan yasan shi ba jaye mishi zaiyi ba, saida ya fita sannan Qasin ya karaso parking space a ransa yana mamakin abunda ya kawo Yarima yanzu,
da sallama ya shigo parlour momi ta amsa masa Mairo ta nufeshi da gudu tana nuna masa kuɗin “yaya ka gani Yarima ya bani duka kuma ni kadai”
kuɗin ya karɓa ya duba yana kokarin zaunawa yace “momi miya kawoshi yanzu kuma”
“jiyara ta kawoshi kuma yace a gaishe ka”
“a gaishe ni? yanzu fa kasa bari yayi na shigo saida na kauce masa”
momi tace “to ai kasan halin kayan ka”
Mairo ta riko hannunsa “yaya kuma harda mumi yaba kuɗi masu yawa”
lakatar mata hanci yayi “ke wai ba ance miki momi ake cewa ba ki daina cewa mumi”
turo baki tayi tana kallon momi “to kuma yaya momi tace mun banida hankali”
kamin Qasin yayi magana momi tace “ai ba kida hankaline Maryam”
kara ɓata fuska Mairo tayi “kaji ko?”
Qasin yayi dariya yace “haba momi Maryam fa nada hankalinta komai na hankali take dan Allah ki daina ce mata mahaukaci”
“Allah ni bana mata ɗaukar masu hankali kaga abunda tayiwa Yarima yanzu?”
“mi ta masa?”
“bata fa sanshi ba daga ganinshi ta tazo a guje ta rumgumeshi ga hannayenta ba kyau har cup ɗin hannunshi ya faɗi”
Qasin ya kalleta “amman ya dakeki ko?”
momi tace “bai mata komai ba dama zan daketa hanani yayi inajin yan k'aurai ne bisan kai harda fa kuɗi ya bata”
murmushi Qasin yayi ya shafa kan Mairo.
yace “ya santa ne shiyasa”
“ina ya santa?”
nan ya bata labari kamar yadda Mairo ta faɗa masa da kuma haduwar da sukayi Dubai Mall,
Momi tace “shiyasa kika rumgumeshi ni ai nayi mamaki yadda naga ya sakar mata fuska harda share mata hawaye”
uhum kawai Qasin yace yana kallon siraj dake saukowa downstairs.
“Maryam faɗa min mi Yarima yake ce miki daya rike miki hannu?”
wani irin ɓata fuska tati ta ɗago tana kallonshi “ni baice min komai ba kawai yace yace yace yana siyomin kayan daɗi kuma kuma yana in yana gaida momi”
taɓe baki yayi “aikin banza”
momi tace “kaga halin nan naks Siraj sam bana sonsa ai kodan girmanka da yayi yaci ake ka gaisheshi amman kaki”
“wlh momi matukar bai sauke wannan girman kan dake tare dashi ba to baza mu taɓa haɗa hanya ba”
cikinsa momi tayi da faɗa “bana fason shashanci Siraj bai girmeka miye abun girman kai a ciki mutun ya tako kafarsa har nan cikin parlour nan ka kasa yi masa magana kaifa da kanka ka buɗe masa kofa ina ruwanka da girman kansa”
murmushi yayi ya nufi kofa “Siraj”
kiran Qasin ne ya juyo dashi “na'am yaya”
“nasan bai fika da komai ba amman ka rika masa magana tunda momi bata so”
kai ɗaga masa ya fice.
candynovels.wordpress.com
© *Khadeeja Candy*
Tags:
Littatafai (Novels)