MAIRO 19

♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*19*

ajiyar zuciya ya sauke ya ciro handkerchief ya kama fuskarta yana share mata hawayen “yi hakuri kinji bazan sake ba daina kuka”
kai ta ɗaga masa tana wani wahalallen numfashi,
kwantarda ita yayi saman kujera “wanta kiyi bachi?”
harta kwanta sai kuma ta ɗago ta kalleshi “yaya karka faɗawa momi kaji?”
kai ya ɗaga mata ya tashi ya fice.

takura kanta tayi saman kujera ta matse guri ɗaya kamar wadda aka cilasta tana matsar kwallah har bachi ya ɗauke ta,

'''   *   *   *   '''

*_2 hours letter..._*
can cikin bachi taji muryar momi da Siraj,
    da sauri ta tashi tana soshe2.
Momi na kallonta taja wani dogon tsaki “haba Maryam ace mutum kana girma kana cin k'asa kamar ki ace inkin dawo makaranta ba kisan ki cire uniform ba saidai ki samu guri ki kwanta dubi kiga har lokacin islamiya ya wuce kuma baki san ki saka uniform kije ba”

ɓata fuska tayi “to momi ba fita kikayi ba kika barni”
nan momi kasa ce mata komai tayi dan takaici in banda tsakin data sakeyi ta nufi kicin,

momi na shigewa Siraj yaja mata kunne “ba wani daman baki son makaranta yar kauye”
fashe masa tayi kuka ta tashi tana aika masa mugayen duduna tana son huce haushinta akansa.

tsawa momi ta katsa mata “wuce ki cire uniform ɗin nan kiyi wanka kila ma ko abinci baki ciba?”
kai ta ɗaga
Momi tace “Allah ya shiryaki maryam wuce kije kiyi wanka duk kika sake yin abunda kikayi yau saina miki shegen duka”
kamar ta fasa kuka ta nufi stairs Siraj na zolayarta,

ta kusan minti 30 toilet ɗin tana wasa ruwa saida taji motsin momi a bedroom sannan ta fara wanka,
koda ta fito momi na zaune saman kujera tana duba wasu matirial da atanfofi.
     kallonta kawai Mairo tayi ta nufi waduraf ta ɗauko wata atamfa red colour riga da saket tasa ko mai bata shafa ba ta janyo k'aton hijab ɗin momi tasa ta shimfiɗa carpet ta soma sallah,

momi na kalle da ita saida ta rama azahar sannan tayi la'asar.
bayan ta sallame ta cire hijab ɗin ta jefar saman bed ta nufi kusa da momi ta zauna,

    “momi kayan waye?”
kyaleta momi tayi saida ta kare danne2 wayar da take sannan ta kalleta “na siyarwane”
shafa kayan ta shigayi “wlh momi suna da kyau suma siyarwa zakiyi?”
momi bata amsa ba ta kama hannunta ta kira sunanta a natse “Maryam”
dariya tayi “na'am momi”
“magana zamuyi ki bani hankalinki kinji banason kisa wasa ki daina dariya kinji?”

wani haɗe fuska tayi saida tasa momi murmushi sai kace wani cartoon ta wani tada kafaɗu “thom ina jinki?”
a natse  momi ta soma mata magana yadda zata fahimta “maryam ki daina abunda kikeyi kinji ba kyau kinga kara girma kike ba ragewa ba ya kamata ki rika sanin ciyon kanki ki daina abunda kike”

“tho ni kuma momi mi nayi?”
ajiyar zuciya momi ta sauke “yanzu fa saida kika rama azahar sannan kikayi la'asar kina ganin kin kyauta?”
kai ta girgiza alamar a a momi tace “tho kingani wadda fa yake haɗa salloli azaba ake masa ba kyau ki daina kinji?”
nan ta ɗaga kai “kuma kinga in kika dawo makaranta maryam basai nace ki cire uniform ba ki rika cirewa duk abunda kika san aikin kine ki rikayi basai nace kiyi ba kinji? ki zama yarinyar kirki”
wata dariya ta rikayi tana kallon momi tana tsutsar leɓenta na kasa,
can dai ta kawarda fuska tace “tho momi na gane koma minene kike nufi”
shafata momi tayi “yauwa yata haka nake so kuma ki dage ki rika karatu ba wasa banda faɗa ko jan magana kinji?”
nan ma kan ta ɗaga ta tashi tsaye “nidai bari naje naci abincin yunwa nake ji”
bata ko tsaya jiran abunda momi za taceba ta fice.

tana saukowa downstairs Qasin na shigowa.
suna haɗa ido ta juya da sauri zata koma hannu yakai ya rikota “ya haka ina zaki?”
upstairs ta rika nunawa “ɗaki zan kwanta ne”
murmushi yayi yaja ta suka nufi kujera bayan ya zauna ya zaunarda ita “baki san ba kyau bachin maraice ba?”
“eh ni ban saniba”
“tho ba kyau ki daina karki sake bachi da maraice”
“tho na daina bazan sake ba”
idonta a kasa take amsa masa dan tsoron kallonsa take.
lura da hakan yasa ya sakar mata hannu yace “tsorona kike ko maryam?”
shiru tayi tana wasa da hannayenta fuskarta ya riko “faɗa min mana tsorona kike ne?”
ɓata fuska tayi ta soma magana “nidai bana son duka in mutun yana dukana tsoronsa nake sosai”

murmushi yayi “tho na daina bazan sake ba ai ban dakekiba”
“eh amman ai kaso ka dakeni dan dai anty mansura tazo ne ka kyaleni”
tana maganar tana wani langwashe langwashen kai da turo baki,

dariya yayi tace “ai ba mansura ce ta ceceki ba daman ba dukanki zanyi ba”
harara ta watsa mishi “kai wlh karya ne tho miyasa ka ɗaga dankon zaka buga min?”
“minene sanki?”
rufe ido tayi tace “wannan wadda kaso ka dakeni dashi”
“bel?”
kai ta ɗaga tana kara matse ido dariya yayi yace “ki yarda maryam bazan iya dukanki ba kawai dai horaki nayi”
kwanta masa tayi saman jiki tana dariya,

“wlh karya ne dukana kaso kayi”
kunnenta riko ya rika murɗawa “ni nake karya?”
dariya ta rikayi tana faɗin “na daina ba kaiba”
haka ya rika wasa da ita soma masa kuka sannan ya saketa ta nufi kicin shi kuma ya fice.

washe gari tunda safe Mairo ta shirya kanta duk abunda momi ta saba mata ita tayiwa kanta,
sosai momi ta jidaɗi da schoolbus ɗinsu tazo har bakin gate momi ta rakata ta buɗe mata motar ta shiga.
hannu ta rika ɗagoma momi har suka fice,

*_2:30pm..._*
ta shigo gidan da sallama ta shiga parlour momi ta amsa mata da fa'ah “wa'alaikissalam yar mama an dawo?”
kai ta ɗaga mata tana cire takalmin makaranta,

daga gurin da take zaune ta jefasu gurin da aka tana da dan ajeye takalmin tana faɗin “momi yau Yarima ya kai mana ziyara a makaranta”
Usman dake zaune kisa da momi yace “da gaske?”
“eh wlh harda chocolate ya raba mana”
momi tace “gurinki yaje ko makaranta gaba ɗaya”
“a a makaranta dai kofa jiya yaje kuma yazo gidan na-”
shiru tayi ta kasa karasawa sai rabon ido take. momi tace “jiya ya zo nan? bayan fitana ko?”
wata dariya tayi “ke momi na tuna mafarkine nayi ba gaske bane”
tashi tayi da sauri ta nufi upstairs “bari naje nayi sallah nayi shirin islamiya”
  tanayi tana waigo momi harta shige.
momi kan daɗine ya isheta tana gani ta fara samun kan Mairo.

© *Khadeeja Candy*

Post a Comment (0)