♡... MAIRO ...♡*
*BY*
*_KHADEEJA CANDY_*
*20*
washe gari ma Mairo ita ta shirya ma kanta komai bayan ta saka safa ta riko schoolbag ɗinta ta nufo downstairs.
da dariya ta sarasa saukowa ta rumgume Qasin dake zaune saman kujera rike da laptop,
aje laptop ɗin yayi yana murmushi ya zaunar da ita saman kafafunsa “maryam har kin shirya?”
ɗagowa tayi tana murmushi “eh kuma ni na shirya kaina”
saukar da ita yayi jin motar makarantarsu ya karɓi jikar hannunta yasa mata,
da sauri momi ta fito kicin rike da kular abincinta tana faɗin “oya karɓi ga abincin ki naji motar ku”
da gudu ta karɓa ta nufi gurin da takalminta suke ta saka harta fice sai kuma ta dawo ta tsaya bakin kofa “momi ba zaki bani komai ba?”
“mi zan baki?”
shiru tayi tana bugun kofar parlour.
hannu Qasin yasa aljihu yana cirowa ya mika mata ɗari biyar,
wata dariya ta saki jikina na rawa ta karɓa tana masa godiya “na gode yaya” kai ya ɗaga mata ta fice da gudu.
ɓata fuska momi tayi tace “Qasin bana so karka sake ka ɗauki kuɗi har ɗari 500 ka bata”
hannu ya ɗaga “shi kenan na daina amman naga kamar bada yawa bane”
cikin faɗa momi tace “tho na dai faɗa maka bana so duk kyautar da ita karta wuce 100 zuwa k'asa”
tana kaiwa nan ta nufi kicin,
da sauri Qasin yace “owk momi yi hakuri ai ya wuce zo kiga wani abu?”
yi tayi kamar bata jishi ba shige kicin ɗin saida ta kare abunda take sannan ta fito.
har lokacin yana zaune ƴyana danne2 sa,
kujerar dake kusa dashi ta zauna “gani ya akayi?”
ɗagowa yayi ya kalleta “momi ɗan ruwan tea ma bazan samu ba?”
taɓe baki momi tayi “au daman jiran kake na ɗauko maka breakfast? inma shine dalilin zamanka nan tho tashi ka koma part ɗinka dan kasan munyi ba'ada dakai tun farko”
dariya yayi “a'a momi bashine ba abu zan nuna miki”
laptop ɗin ya ɗauko ya ɗora saman jikinta “kinga wani design ɗin wata kwangila da za'ah ba kanfaninmu”
duba momi ta shigayi tana faɗin “amman kan abun da girma sosai mi za a gina haka?”
“wani kanfani suke so a gina musu na sarrafa motoci _JAMES GLOBAL AUTOMOBILES_ sunan kanfanin shine na farko da zai kafa branch a Nigeria”
momi tace “aiko dasun kyauta muma mu ɗan samu cigaba kuma matasan mu su samu aiki”
“sosai ma momi kinga in aka ginashi mutun kusan ɗari biyar zasuyi aiki karkashin su kinga ai an ɗan rage kuma kanfanin sun iya motoci ana son motocinsu sosai sune zakiga J.G.A mutunin ɗan amerika ne”
momi tace “amman naji daɗi to kai zaka gina musu gurin ne?”
“tho haka ake tunani amman dai ba ni kaɗai bane mu uku aka kaimusu zasu zaɓa ne saisu bada kwangilar ga wadda suka yarda da aikinsa amman dai mutane da yawa ni suke cewa saboda kanfanin fitaccen kanfanine kuma muna aiki babu kissa ciki”
murmushi momi tayi “tho ai haka ake so Allah ya taimaka yasa ka samu”
“amin momi dan gaskiya zamu samu kuɗi masu yawa”
“to Allah ya yarda ya taimaka”
“amin”
tashi yayi rike da laptop ɗin yana kallon “bari naje can na karya”
kai momi ta ɗaga mishi “da yafi”
murmushi yayi ya fice.
*_7pm..._*
Mairo na zaune parlour kasan carpet ita da Siraj yana duba littafanta na makaranta sai zolayarta yake tana masa kuka yana sa ta karanta gurinda bata iyaba yayi mata dariya ita kuma ta buga masa fillo. suna haka sukaji an taɓa kofa duk juyawa sukayi suna kallon kofar,
cike da takama Yarima ya shigo ba tare da yayi sallama ba ya nufo gurinda suke,
wani irin haɗe fuska Siraj yayi kamar bai taɓa dariya ba,
wannan karon Mairo batayi unkurin tarboshi ba ido kawai ta sakar masa tana dariya.
da murmushi ya karaso kusa da ita tashi Siraj yayi tsaye da niyar tafiya tunowa da magagganun momi yasa ya kalli yarima yace “sannu da zuwa”
banza ya masa yana tsutsar lips ɗinsa.
juyawa Siraj yayi cike da bachin rai ya fice,
hannu Mairo ya riko yana murmushi ya nufi kujera suka zauna tare.
kallonsa tayi tace “ba kaji Siraj yana mska magana ba?”
lakatar mata hanci yayi “na jishi bana jin amsa masa ne”
murmushi tayi gyaɗa masa kai,
wasa ya shigayi da hannayensa yana faɗin
“pretty gal ya maranta?”
“lafiya kalau”
“ina momi?”
“tana ɗaki na kirata?”
hannu yasa yana taɓa lips ɗinta “a a karki kirata”
saida ya ɗaga kansa ya kalli upstairs sannan ya kalleta yace “gurinki nazo kinsan munyi dake zan saki abu ko?”
kai ta ɗaga “eh kuma kace zaka bani kuɗi kuna kace zak-”
rufe mata baki yayi da sauri jin motse saukowar mutun downstairs,
saida yayi mata alama da tayi shiru sannan ya juya da murnushi yana kallon momi.
“Yarima yanzu ake tafe?”
“eh momi ya wunin gidan?”
taka kokarin zaunawa tace “lafiya kalau maryam baki ɗauko masa abun sha ba?”
war tayi da ido tace “lahh mantawa nayi bari na ɗauko”
tana sauka ya riko hannunta ya tashi tsaye “a a momi barshi kawai yanzu zan wuce”
“da wuri haka?”
“eh kinga an kira sallar isha kuma daman biyowa kawai nayi naga Maryam”
da ɗan mamaki momi tace “owk tho a gaida gida”
hannu yasa aljihu ya ciro dubu 20 ya aje mata “ayi hakuri da wannan momi”
murmushi momi tayi “Yarima kenan Allah dai ya amfana”
baice komai ba yaja hannun Maryam suka fice,
motarsa ya buɗe mata ta shiga bayan ya rufe ya zagayo shima ya shiga.
“ina zamu?”
tambayar data fara jefa masa kenan tana kallonshi,
baice mata komai ba yasa hannu baya ya ɗauko laptop ya ɗora mata saman jiki “kinga wannan abun?”
“eh”
“kin taɓa ganinta?”
“eh sunanta kwanfuta”
mirmushin jindaɗi yayi “good wa kika taɓa gani da irinta?”
“malamin makarantarmu da yaya”
“tho kinsan mi nake ao dake?”
kai ta girgiza “a a”
“ta yaya nake son ki ɗauko min”
da sauri tayi waje da ido ta rufe baki “kaikai nidai babu ruwana baya so fa ina taɓa mishi kaya”
“ke mayarwa zanyi kawai inason na arane na ɗanyi wani abu sai na baki ki mayar”
lake kafaɗa tayi “a a gaskiya saidai nace ya aro maka”
haɗe mata fuska yayi “a a karki kuskura kice masa haka bazai bayar ba kuma inma yaji dukanki zaiyi kuma nima na ɓata dake”
hannu yasa ya ɗauko wata leda dake bayan ya mika mata “kinga kayan daɗi nan na siyo miki kuma gobe zan karo miki wasu kullum zan rika siyo miki kuma na baki kuɗi amman fa sai in kin aikata abunda nace”
shiru tayi tana tunani kamar ta fasa kuka ta kalleshi tace “amman inna ɗauko cewa zaiyi mi zanyi da ita”
“no ai bazaki bari ya gani ba a boye zaki ɗauko karki yarda kowa ya gani koda kuda ne”
“tho inna ɗauko ina zan ɓoye?”
shiru yayi yana kallonta kamin yace
“ke bakisan gurin da zaki ɓoye ba?”
“eh duk gurinda zan ɓoye gani za ayi”
“tho ki kaɗa rijiya”
“kai rijiya?”
“eh koki jefar wani gurin innazo sai ki faɗamin na ɗauko”
“ba zai lalace ba?”
“ba zaiyi komai ba kinji”
kai ta ɗaga mishi sosai yaji daɗi ya shafa kanta “good pretty gal”
“amman mi zakayi da ita”
idonsa ya shiga susa kamar wadda abu ya faɗawa “am zan ɗan ɗauki wani abune a ciki na cofa sai na baki ki mayar kinga bazai gane ba ko?”
da mirmushi ya karasa maganar itama tayi masa murmishin karfin hali,
kuɗi ya ciro masu yawa ya mika mata “gashi ki siye duk abunda kike so amman kinsan bazaki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake ba ko”
“eh bazan faɗa ba”
“good kuma tsakanin gobe sa jibi nake son ki ɗauko min ita”
kai ta ɗaga mishi,
daga nan ya mika hannu ya buɗe mata motar shima ya buɗe suka fito tare.
Qasin na tsaye bakin kofa yana kallonsu yana rumgume da hannayensa fuskarsa a haɗe,
faɗuwa gaban Mairo yayi da sauri ta juya ta riko hannun Yarima ta soma kuka “nidai bazan iya zuwa ba ga yaya can yana kallona”
mirmushi yayi yaja hannunta suka nufi kofar parlour.
har suka isa Yarima bai kalli gefen da Qasin yake ba,
ita kadaice ke masa kallon tsoro jikinta har wani ɓari yake, da kansa ya buɗe mata kofar data shiga yayi mata byebye yana murmushi hannu itama ta ɗago mishi sannan ya rufe kofar,
yana juyowa Qasin yace “ka bani kunya ka kuma zubar da girmaka momi bata taɓa yiwa yayanta gurɓatacciyar tarbiya ba kuma bana tunanin za'a samu matsala a maryam dan haka ta banbanta da sauran matan da kake gani.
maryam karamar yarinya ce in zakayi sama kayi kasa ba za ah aura maka itaba balle baka daman lalata mata rayuwa dan haka banga abunda zai haɗaku ba”
yana kaiwa nan ya juya ya shigewarsa parlour.
kasa tafiya Yarima yayi sosai maganganun suka ɓata masa rai sai wani busar da iskar baki yake,
_ɗan iskane ni Qasin na karshe har yanzu baka gama sanina ba zan nuna masa true color na_
a zuci yake wannan zancen yana wani kashe ido.
candynovels.wordpress.com
Tags:
Littatafai (Novels)