OBASANJO SHI NE FARKON WANDA YA FARA NAƘASA AREWA

*OBASANJO SHINE FARKON WANDA YA FARA NAKASA AREWA*

Atiku Abubakar yace idan an zabeshi zai daura daga inda maigidansa tsohon shugaban Kasa Olosegun Obasanjo ya tsaya.. wannan bayanin Atiku ne ya furta da bakinsa.

To dai abinda aka sani inda Obasanjo ya tsaye da ayyukansa lokacin da yake shugabancin Nigeria gasu kamar haka a takaice:

1- A lokacinsa ne aka nakasa duk wani kamfani da yake arewa !

2- A lokacinsa ne aka dukufar da karfin wutar lantarkin arewa ta yanda cikin sauki babu wani kamfani da ya isa yayi aiki a arewa dubbannin matasa su samu ayyukan yi !

3- A lokacinsa ne aka kifar da Mai Martaba Sarkin musulmin Nigeria a jirgi aka hallakashi tare da wasu manyan arewa !

4- *A lokacinsa ne aka tattara hazikan sojojin arewa da zasu iya kaiwa babban matsayi aka musu ritayar dole daga aiki domin a raunata karfin 'yan arewa a gidan sojin Nigeria !*

5- A lokacinsa ne aka kwashe manyan kayan yakin rundinar sojin Nigeria daga arewa aka mayar dasu can yankinsa saboda wasu boyayyun dalilai nashi !

6- Obasanjo shine farkon wanda ya fara cewa 'yan arewa kaska ne, 'yan arewa sune matsalar Nigeria !

7- Obasanjo shi ya kawo Marigayi Umaru Musa 'Yar adua saboda likitoci sun tabbatar masa ba zai jima a duniya ba, sai ya kawo yaronsa Jonathan ya masa mataimakin shugaban Kasa, karshe ta Allah ta kasance akan Umar Musa. Jonathan ya zama shugaban Kasa wanda inda haka bai faru ba, to da bamu fuskanci bala'in kungiyoyin ta'addanci da aka turo don a ruguje arewacin Nigeria kasar musulunci ba.

8- Obasanjo shi ya bada shawara ga Goodluck Jonathan cewa idan yanaso ya shimfida mulki irin wanda yakeso, to ya saki kudi ga shugabannin arewa zaiyi yadda yaga dama da Nigeria, kuma haka akayi, a tarihin kafuwar Nigeria ba'a taba yin shugaban da ya saki kudi ga shugabannin arewa ba kamar Jonathan, ta karkashin kasa kuma yana dasa mutanenshi domin su kwace madafun ikon kasar, da ya rufe bakin manyanmu da kudi, sai aka kyale 'yan ta'adda sukaci karensu babu babbaka, idan arewa ta rushe already sun gina manyan gidaje a kasashen waje zasu gudu tare da iyalansu.

Wannan a takaice shine tsarin ayyukan Obasanjo ga arewa, Atiku yace idan yaci nasaran zama shugaban Nigeria zai cigaba daga inda maigidansa Obasanjo ya tsaya, don haka Atiku Abubakar bai camcanta mu zabeshi ba indai muna son kanmu da arziki !

Yaa Allah Ka sanya katangar karfe tsakanin 'yan arewa da wadannan mutane.
Post a Comment (0)