WATA MATA MAI HIKIMA

Mushadariya daga deen
WATA MATA MAI HIKIMA

Wata matace anan kasar hausa tashiga wayar mijinta bangaren Facebook taga irin firar da yake yi da wata mace
Sai take ta tunanin wacce hanya zatabi domin ta rabasu cikin sauki batareda shi kansa ya fahimta ba ga hanyar data dauka:
1- Tabude sabon account a Facebook dasuna namiji
2- Ta turawa mijinnata neman abokantaka wato [friend request] kuma ya amsa
3- Tayi copy na dukkan text din dayayi da waccan dama
4- Suka fara gaisawa ta gabatar da kanta da cewa ni dan kungiyar ISIS ne wanda anan kukafi sani da BOKO HARAM kuma naga duk irin sakonnin daka turowa matata gasu sai ta turamasa da sakonnin nan gaba daya
5- Tace idan baka daina chatting da matata ba wallahi sai na maka yankan Rago
6- Nasanka sunanka wane anai maka inkiya da wane, sunan mahaifinka wane, sunan mahaifiyar ka wance, kanada ya'ya guda kaza,ga sunansu ta lissafo sunan yaransa dukka kuma kanada sana'a iri kaza Sannan kana fita lokaci kaza kadawo lokaci kaza Sannan kanada abokai wane da wane. Mune members a garinku idan nasake ganin text dinka koka kirata awaya ko chatting wallahi saina maka yankan Rago.
Matar tashi tace ina ganinsa yana karantawa sai zufa yake yana share gumi yana fadin innalillahi wa inna ilaihi raji'un, idan na tambayeshi meke faruwa sai yace babu komai anan take ya share Facebook dinsa da whatsapp dinsa da dukkan wata social media dinsa ya goge yana zufa yana mai mai ta innalillahi wa inna ilaihi raji'un
Karshe dai gari na wayewa yaje ya saida wayar a kasuwa ya sayi wadda bata charting sai dai yayi kira akirashi kawai Sannan yacewa matar tasa dan Allah daga yanzu dakinji anyi kiran sallah kitasheni kowanne lokaci ne.
Tace wallahi daga lokacin sallah bata wuceshi ya dinga addininsa inda yakamata bakamar sanda charting yana dauke hankalin saba.


1 Comments

Post a Comment