_*🕌Islamic Post*_
_عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله ﷺ قال: *”من قام رمضان إيمانًا واحتسابًا غفر له ما تقدم من ذنبه“* متفق عليه._
_An kar6o daga Abu Huraira (r.a), hakika Manzon Allah (ﷺ) ya ce: *“Duk wanda ya tsayu a Ramadan, ya na mai imani, da neman ladan Ubangiji, to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.”* Bukhary da Muslim._
.
.
_Wannan hadisin na kwadaitar da mu falalar da ke cikin watan Ramadan ne idan mun yi abubuwan da ake so a cikin sa._
_Manzon Allah (ﷺ) ya na nufin duk wanda ya tsayu a cikin watan Ramadan da imani, ya kasance kuma ba komi ya sa ya tsayu ba sai don biyayya ga Allah (ﷻ) da neman lada daga gurin Shi Shi kadai, kuma ya dawwama a kan hakan, ya na salloli (na nafila) cikin tsoron Allah. Kuma ya yawaita karatun Alqur'ani da Tasbihi da Istigfari a cikin watan. To duk wanda ya aikata hakan, Allah zai gafarta masa zunubansa tsakaninsa da shi wadanda suka gabata._
_'Yan uwa Musulmai! Wannan ba karamar garabasa ba ce, don haka mu yi kokari mu dabi'antu da wadannan dabi'u a cikin wannan watan mai albarka._
_Ya Allah Ka gafarta mana zunubanmu 👏🏽_
_Dan uwanku a Musulunci:_
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
*08166650256.*