YAU MA KUNU ZA'A SHA

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA �*
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_

*DRS NA 016*

*Yau Ma Kunu Za a Sha*
Wata amarya ce aka kai ta dakinta. Aka dauki wani dan lokaci ‘yan uwanta suna zuwa suna taya ta girki. Daga bisani da suka rage sai �ta fara yin girki da kanta. Ango kuwa sai santi yake yi saboda dadin abincinta.
Watarana kawai sai ya so ya birge abokansa, ya nuna masu irin sa’ar mata da ya yi wacce ta iya girki. Don haka sai ya sanar da ita tun da dare cewa, gobe da rana zai zo da abokansa don su ci abinci a cikin gidansa.
Da aka wayi gari zai fita ya sake tuna mata cewa, yau fa akwai baki. Sannan ya kawo kuxin cefane ya ba ta, ya fita zuwa nasa sha’ani.
Ita kuma saboda kuruciya bayan da ta gama dama kunun safe sai ta kwanta ta yi ta bacci abinta. Tashin ta kawai sai ta ji ladan yana kiran sallar azahar. Kamar ba a yi komai ba sai ta share ta ci gaba da sha’aninta.
Jim kadan Ango ya shigo gida cikin murna da doki ya yi sallama ta amsa masa. Sai kawai ya ga ta canja fuska. Lafiya kuwa? Ta ce, ba
komai. Kin kammala aikin abincin dai? “Ni fa kunu kawai na yi”.
“Kunu”? Ta ce, “Eh, shi nake sha’awar sha”. Bai ce ma ta uffan ba, ya kada kai ya fita.
Amarya dai ta san ba ta yi daidai ba. Amma kuma tana jiran hukuncin da maigida zai yanke mata. Amma kuma me zai iya yi a yanzu? Farawa da iyawa, amarya da ragga! Da marece ya yi ta neme
shi kudin cefane, sai ya ce “Ai kunu za mu sha”. A ranta ta ce, wannan kam ai ba komai. Ya ma fi saukin damawa. Aka wayi gari aka sha kunu, da rana kunu, da dare ma kunu. Haka aka kwana uku duk sadda ta nemi kudin cefane sai ya ce ma ta “Ai kunu za mu sha”. Da ta gaji da
hakuri da shan kunu sai ta arce zuwa gidansu. �
Da mahaifinta ya gan ta a gida sai abinya ba shi mamaki. Nan take ya buga ma mijinta waya yana tambayar sa ko lafiya ya kawo ta gida a yanzu? Ya ce, Baba ni ma ban san ta tafi ba. Amma dai ka ji ka ji yadda aka yi. Sai ya ce, to shikenan, ka bar ta kawai ba sai ka zo
daukar ta ba. Da lokacin fitar sa ya yi sai uwargida ta nemi kudin cefane, sai ya ce “Ai gidan nan yau kunu za a sha”. Da yamma ma ya
ce “Kunu za a sha”. Haka suka yi wasu kwana biyu tana shan kunu a
gidan iyayenta bayan ta kwana uku shi take sha a gidan mijinta. Da ta ga cewa, babu sarki sai Allah sai ta sulale ta komawar ta gidan mijinta.
Shi kuma sai ya yi kamar bai san akwai wani abu ba, ya yi maraba da ita, suka gaisa, sannan ya ce ta tashi ta dora masa ruwan zafi yana son
zai sha kunu! Ai kuwa sai ta fashe da kuka. Sannan ta durkusa tana ba shi hakuri tana rokon gafarar sa. Suka shirya, ba ta sake yin irin
wancan ganganci ba.

*Darussa:*
▶ Akwai hanyoyi da yawa na magance matsala ba sai da fushi ko zagi ba.


▶ Maigida shi ne takobin daga. Idan babu hadin kansa gida ba zai yi kyau ba.


▶ Aure akwai dadi, amma fa in an dace da iyaye masu mutunci. �
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.

Post a Comment (0)